2019: Babu makawa Buhari zai yi nasara – Dattawan APC

2019: Babu makawa Buhari zai yi nasara – Dattawan APC

- Kungiyar dattawan jam’iyyar APC, a jihar Plateau sun bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da na Gwamna Simon Lalong za su yi nasaraa zabe mai zuwa

- Daga Buhari har Lalong dai na neman yin tazarce ne a zabe mai zuwa

- Tsohon mataimakin gwamnan jihar Plateau, Akun ya bayyana cewa dandazon mutanen da suka hallara a wajen kaddamar dea kamfen din APC a jihar a ranar Juma’a 4 ga watan Janairu alamu ne da ke nuni ga nasara

Kungiyar dattawan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a jihar Plateau sun bayyana cewa nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari da na Gwamna Simon Lalong a zabe mai zuwa “tabbass ne”.

An tattaro cewa Buhari da Lalong na neman goyon bayan jama’a domin samun damar zarcewa a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu da na 2 ga watan Maris.

Cif Jethro Akun, shugaban kungiyar, reshen Plateau ta tsakiya ya bayyana haka a ranar Laraba, 9 ga watan Janairu a Jos, yayinda yake kaddamar da wani taro da kungiyar ta shirya.

2019: Babu makawa Buhari zai yi nasara – Dattawan APC

2019: Babu makawa Buhari zai yi nasara – Dattawan APC
Source: Depositphotos

Akun wanda ya kasance tsohon mataimakin gwamnan jihar Plateau ya bayyana cewa dandazon mutanen da suka hallara a wajen kaddamar dea kamfen din APC a jihar a ranar Juma’a 4 ga watan Janairu alamu ne da ke nuni ga nasara.

Yace sun gudanar da taron ne domin hada kai wajen ganin nasarar jam’yyar a zabemai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta sanya ranar fara sauraron karar haramtawa shugaba Buhari takara a zaben 2019

A wani lamari na daban, mun ji cewa ayinda guguwar zaben 2019 ke dada hurowa, yan takara da jam’iyyunsu na ci gaba da kokarin ganin sun samu karin magoya baya domin ganin sun kai labari, hakan ce ta kasance ga jam’iyyar APC a Gombe inda ake ganin tana kara yin karfi bayan wani tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar Democratic Peoples Party (DPP), Nafiu Bala Gombe ya sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Haka zalika akalla mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne suka kaddamar da goyon bayansu ga APC a karamar hukumar Shongom.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel