Zargin yana tu'ammali da barayi: Shugaba Buhari ya wanke kansa

Zargin yana tu'ammali da barayi: Shugaba Buhari ya wanke kansa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalubalanci zargin da akewa jam'iyyar APC

- Ana zargin jam'iyyar da kyale duk wani mai laifi matukar ya koma jam'iyyar

- Shugaban yace duk wanda yasan ya taba hana wata cibiya hukunta mai laifi toh ya fito ya bayyana

Zargin yana tu'ammali da barayi: Shugaba Buhari ya wanke kansa

Zargin yana tu'ammali da barayi: Shugaba Buhari ya wanke kansa
Source: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maida martani game da zargin jam'iyyar APC da ake na kare mahandaman yan siyasa in har suka koma jam'iyyar.

Shugaban kasar yace ba wanda zai kyale matukar akwai shaidu kwarara akan almundahanar.

Zargin cewa yakin rashawa na bangare daya ne a gwamnatin, tare da kalubalen cewa hukumar yaki da rashawa sun maida hankali akan jam'iyyar adawa kuma tare da kyale duk wanda ya koma jam'iyyar APC.

Jam'iyyar ta karyata wannan ikirarin ta hanyar bada misali da tsofaffin gwamnoni- Joshua Dariye na jihar Filato da Jolly Nyame na jihar Taraba- wadanda suka koma jam'iyyar APC yayin da suke fuskantar shari'a.

Komawar tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP ta arewa, Babayo Gamawa, jam'iyyar APC a ranar talata bayan da yana fuskantar shari'ar zargin shi da akeyi da almundahanar Naira Miliyan 500.

A wata tattaunawa da majiyar mu tayi da shugaban kasar, yace bai umarci wata cibiyar yaki da rashawa ba da kada ta binciki wani shugaba ba da ya dawo jam'iyyar APC ba.

Akan maganar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, wanda wasu ke zargin ya bar jam'iyyar PDP ne don gudun tuhumar da za a mishi wanda shugaban kasa yace wadannan zargin bai dace ba.

Hukumar yaki da rashawa tana zargin Mista Akpabio da almundahanar Naira biliyan 108.1, a lokacin da take shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa. Hukumar yaki da rashawan ta kama shi kusan sau biyu.

A watan Augusta na 2018 ne sauka daga matsayin shi na shugaban marasa rinjaye na majalisar inda ya koma jam'iyyar APC.

GA WANI: Gwamnati ta warware aure 48 wanda aka yi wa mata kanana a arewa

Duk da bai yi maganar Hukumar yaki da rashawa ba a cikin dalilan shi na komawa jam'iyyar APC ba, akwai hasashen dalilan da yasa ya bar tsohuwar jam'iyyar shi. Dalilin da wasu suka yi ta hasashe shine gudun fuskantar shari'a.

Daga nan babu wanda ya kara jin maganar almundahanar shi ba.

Da aka tambayi shugaban kasar akan maganar Akpabio sai yace ba a dagawa duk wanda aka kama da laifi kafa.

"Wannan zargin ba a kyauta ba kuma barazana ne ga nagarta ta. Bana dagawa kowa kafa sai dai idan banda shaida. Bana tunanin nace a kyale Akpabio akan ya dawo jam'iyyar APC," yace.

"Bana tunanin na cewa EFCC, ICPC, yan sanda ko wata cibiya da ta kyale wani mai laifi. Banyi haka ba kuma idan nayi na kalubalance ku da ku bayyana," inji shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel