Gwamnatin tarayya ta amince da sabbin jami’o’i 4 (jerin sunaye)

Gwamnatin tarayya ta amince da sabbin jami’o’i 4 (jerin sunaye)

- Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kan su a kasar

- Ministan ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman kwamitin zantarwa da ma’aikatar ta yi

- Jami’o’in da aka amince da su guda hudu ne

Rahotanni sun kawo cewa a zaman da bangaren zartarwa ta yi a yau Laraba, 9 ga watan Janairu, gwamnatin Tarayyar kasar ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kan su a kasar.

Ministan ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman kwamitin zantarwa da ma’aikatar ta yi.

Gwamnatin tarayya ta amince da sabbn jami’o’i 4 (jerin sunaye)

Gwamnatin tarayya ta amince da sabbn jami’o’i 4 (jerin sunaye)
Source: UGC

Ga jerin sunayen jami’o’i da aka amince da su mun kawo maku a kasa:

1. Jami’ar Greenfield a jihar Kaduna

2. Jami’ar Dominion a Ibadan jihar Oyo

3. Jami’ar Trinity a jihar Ogun

4. Jami’ar Westland a Iwo jihar Osun

KU KARANTA KUMA: Zan ba mata da matasa ayyukan yi idan na zama shugaban kasa - Atiku

A lissafe adadin jami’o’i masu zaman kan su a kasar ya kai 79 kenan.

Kafin amincewa da sabbin jami’oi hudu da aka yi yau, Najeriya na da jami’o’i mallakar gwamnatin tarayya 40 ne, Jami’o’i mallakar gwamnatocin jihohi 45 da masu zaman kansu 75.

An fara kafa jami’o’i masu zaman kan su a kasar nan ne a 1999 in da aka kirkiro da jami’o’i 3 da suka hada da jami’o’in Babcock, Igbinedion da Madonna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel