Kotu ta sanya ranar fara sauraron karar haramtawa shugaba Buhari takara a zaben 2019

Kotu ta sanya ranar fara sauraron karar haramtawa shugaba Buhari takara a zaben 2019

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Abuja, ta sanya ranar 21 ga watan Janairun 2019, domin fara sauraron karar haramtawa shugaban kasa Muhammadu Buhari takara a babban zaben kasa da za a gudanar a bana.

Karar da sanadin masu korafin ta, Mista Kalu Agu, Labaran Ismail da kuma Hassy El-Kuris, na zargin shugaban kasa Buhari da shirga karya dangane da takardun shaidar sa ta kammala karatu yayin gabatar da fam din sa na bayyana kudirin takara ga hukumar zabe ta kasa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, zantuka sun gudana kan harsunan al'umma a nan gida Najeriya da kuma kasashen ketare kan dambarwar takardar shugaba Buhari ta kammala karatun sa na sakandire wato WAEC.

A watan Nuwamban da ya gabata ne hukumar da ke shirya jarabawar kammala manyan makarantun sakandire ta kasashen yammacin Afirka (WAEC) ta mika wa shugaban kasa Buhari takardar shaidar kammala sakandire.

Kotu ta sanya ranar fara sauraron karar haramtawa shugaba Buhari takara a zaben 2019

Kotu ta sanya ranar fara sauraron karar haramtawa shugaba Buhari takara a zaben 2019
Source: Depositphotos

Jaridar Vanguard tun a bara ta ruwaito cewa, babbar hedikwatar hukumar WAEC da ke kasar Ghana, ta ce ba ta da wata shaida cikin ma'adanar ta da ke nuni da cewa shugaban kasa Buhari na da rajistar jarabawar sa ta kammala sakandire kamar yadda ya yi ikirari.

A sakamakon wannan lamari, masu korafi su ka shigar da karar shugaba Buhari har gaban kuliya domin haramta ma sa takara bisa ga tanadin sashe na 31 cikin kudin tsari na babbar hukumar zabe ta kasa wato INEC.

KARANTA KUMA: Zaben 2019 zai zama haramiyar gwamnati idan ba ta tabbatar da mafi karancin albashin ma'aikata ba - Kungiyar Kwadago

Ma su korafin uku sun kuma roki babbar kotun tarayya akan umartar hukumar zabe ta kasa da ta gaggauta tsame sunan shugaba Buhari daga jerin 'yan takara na jam'iyyar APC da za su fafata yayin zaben kasa da zai gudana a watan gobe.

Alkalin kotun, Mai shari'a Ahmed Muhammad, ya kayyade ranar 21 ga watan Janairu na wannan shekarar domin fara sauraron karar tare da bayar da umarnin ankarar da hukumar zabe da kuma jam'iyyar APC dangane da wannan babban lamari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel