2019: Jam’iyyar PDP tayi watsa-watsa da Asiwaju Tinubu saboda sukar Atiku

2019: Jam’iyyar PDP tayi watsa-watsa da Asiwaju Tinubu saboda sukar Atiku

Mun samu labari daga jaridar Vanguard cewa jam’iyyar PDP tayi kaca-kaca da Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC bisa kalaman da aka ji yana yi a kan ‘dan takarar ta watau Atiku Abubakar.

2019: Jam’iyyar PDP tayi watsa-watsa da Asiwaju Tinubu saboda sukar Atiku

PDP ta fadawa Asiwaju Tinubu ya daina taba 'Dan takarar ta Atiku
Source: Facebook

Jam’iyyar PDP ta maidawa babban jigon na jam’iyyar APC martani ne ta bakin kwamitin da ke yakin neman zaben Atiku Abubakar a 2019. PDP ta ba Tinubu shawara ya rika magana kamar yadda aka san sauran Dattawan kasar.

Kola Ologbondiyan wanda shi ne Darektan yada labarai na yakin zaben Atiku a jam’iyyar PDP yayi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya rika tauna maganganun da yake yi a fili a matsayin da yake domin kuwa Duniya ta na kallon sa.

Ologbondiyan ya fadawa tsohon gwamnan na Legas cewa bai kamata ya rika kokarin ci wa Atiku mutunci saboda alakar siyasa wanda ba ta kai ta kawo ba. Jagoran na PDP yace Atiku mutum ne da ake ganin darajar sa a Najeriya.

KU KARANTA: Dole in yabawa aikin gwamnatin APC inji wani 'Dan adawan Buhari

PDP dai ta gargadi babban jigon na jam’iyyar ta APC da ke mulki a Najeriya cewa ya daina sakin baki yana magana babu kan-gado. Jam’iyyar ta gargade sa da cewa ya daina yaudarar kan sa da cewa zai samu mulkin kasar a 2013.

Jam’iyyar adawar tace ya kamata irin su Bola Tinubu da aka sani da gwawarmaya su fito ne su yaki Buhari, su kuma marawa Atiku Abubakar baya a zaben da za ayi a bana domin ganin an cire Najeriya daga kangin da aka jefa ta.

Tinubu dai yace ya zabi Muhammadu Buhari ne saboda irin tsabar gaskiyar sa, wanda a cewar sa, Atiku Abubakar bai da ita. PDP dai tace wannan batun gaskiyar shugaban kasar, tatsuniya ce kurum ake yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel