Sojoji sun kwato manyan bindigu 45 daga hannun 'yan ta'adda a jihar Arewa, hoto

Sojoji sun kwato manyan bindigu 45 daga hannun 'yan ta'adda a jihar Arewa, hoto

- Rundunar soji na Operation Wild Stroke da ke yaki da masu aikata laifuka a jihohin Nasarawa, Benue da Taraba tayi baje kolin makaman da ta kwato a Nasarawa

- Kwamandan rundunar, Janar Adeyemi Yekini ya ce sun samu gaggarumin nasara wurin yaki da bata gari a jihohin

- Janar Adeyemi ya ce bayannan sirri da rundunar sojin ke samu ne ya ba su ikon gano mabuyar 'yan ta'addan na Bassa a jihar Nasarawa

Hukumar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kwato bindigu 45 daban-daban da kuma tarin wasu makamai masu yawa daga hannun 'yan ta'addan Bassa da ke sansaninsu a Zwere da ke karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa.

Kwamandan atisayen Operation Wild Stroke da ke kula da jihohin Nasarawa, Benue da Taraba, Manjo Janar Adeyemi Yekini ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Sojoji sun kwato bindigu daga hannun tsageru a jihar Nasarawa

Sojoji sun kwato bindigu daga hannun tsageru a jihar Nasarawa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An dakatar da sarakuna biyu a Zamfara saboda alaka da 'yan bindiga

"Mun kwato bindigu daban-daban guda 45 da kuma wasu muggan makamai 701 du suka hada da Sub machine gun guda 1, bindiga kirar Najeriya guda 39, G3 rifle guda 2, bindigar hannu guda 3, jigidan alburusai na G3 guda 5, alburusan revolver guda 4, Kayan sojoji guda 3, wayoyin salula, da layyu da dai sauransu," inji shi.

A yayin da ya ke gabatarwa manema labarai makaman a Lafia, Janar Adeyemi ya ce, "Muna gabatar muku da wannan makaman ne domin mu bayyana muku nasarorin da Opertaion Wild Stroke ya samu sakamakon bayanan sirri da muke samu.

"An kafa wannan rundunar ne watanni takwas da suka gabata domin kawo karshen kashe-kashen makiyaya keyi da wasu kungiyoyin 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihohin Nasarawa, Benue da Taraba.

"Mun kwato makamai masu yawa da bindigogi kuma mun damke mutane da dama da ake gudanar da bincike a kansu cikin watanni takwas da suka gabata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel