Yawan dalibai, yan kasuwa, ma'aikatan gwamnati, iyaye mata , manoma, da za suyi zabe a 2019

Yawan dalibai, yan kasuwa, ma'aikatan gwamnati, iyaye mata , manoma, da za suyi zabe a 2019

A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta gabatar da jimilla ta adadin al'ummar kasar nan da suka shiryawa babban zabe na 2019. Hukumar ta ce 'yan Najeriya 84,004,084 ke da rajista ta cancantar kada kuri'u a zaben.

Rahoton hukumar ya bayyana yawan mutanen da ake kyautata zaton zasu kada kuri’a a zaben da za’a gabatar a wata Febrairu da Maris na wannan shekara. A cikin wadanda zasu kada kuri’arsu sune Daliban ilimi, ma’aikatan gwamnati, matan aure, masuna, manoma, yan kasuwa, masu aikin hannu, da kananan yan kasuwa.

KU KARANTA: Yayinda yankin Arewa maso yamma tafi yawan kuri’u, Yankin Inyamurai ce mafi karancin kuri'u a 2019 – Rahoton INEC

Ga adadinsu:

1. Kananan yan kasuwa: 7,568,012

2. Masu aikin hannu: 4,478,202

3. Manyan yan kasuwa: 10,810,006

4. Ma’aikatan gwamnatin: 5,038,671

5. Manoma da masuna: 13,630,216

6. Matan aure masu kula da gida : 11,844,079

7. Masu rike da makamun gwamnati: 2,292,167

8. Dalibai: 22,320,990

9. Sauran jama’a: 6,021,741

Wannan lissafi ya nuna cewa adadin dalibai ya fi kowani bangare yawa sannan manoma da masuna, sannan manyan yan kasuwa, sannan matan aure, sannan kananan yan kasuwa, sannan masu rike da kujerun gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel