Yanzu yanzu: ASUU ta ce bata cimma wata matsaya da gwamnatin tarayya ba

Yanzu yanzu: ASUU ta ce bata cimma wata matsaya da gwamnatin tarayya ba

- ASUU ta karyata wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta yi na cewar ta cimma yarjejeniya da kungiyar dangane da bukatun da ta gabatar, inda sanarwar karyar banza ce

- ASUU ta ce har yanzu tagawar da ta wakilce ta a taron ba ta bayyana nata matakin na karshe kan hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke a wajen taron ba

- ASUU ta jaddada cewa ya zama wajibi a kammala yarjejeniyar a rubuce, tare da matakan da kuma hukuncin da za a dauka idan aka saba yarjejeniyar

Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU, a ranar Laraba, sun karyata wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta yi na cewar ta cimma yarjejeniya da kungiyar dangane da bukatun da ta gabatar, inda kungiyar ta ce wannan sanarwa ta gwamnatin tarayya karyar banza ce kawai.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya karyata wannan sanarwa ta gwamnatin tarayya a cikin wata zantawa da jaridar TribuneOnline.

A cewarsa, har yanzu ba a cimma wata matsaya tsakanin bangarorin biyu ba, sakamakon tagawar da ta wakilci ASUU a taron ba ta bayyana nata matakin na karshe kan hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke a wajen taron ba.

KARANTA WANNAN: Cikin shekaru 3: Yan Nigeria 104 suka mutu a wajen aikin Hajji - NBS

Yanzu yanzu: ASUU ta ce bata cimma wata matsaya da gwamnatin tarayya ba

Yanzu yanzu: ASUU ta ce bata cimma wata matsaya da gwamnatin tarayya ba
Source: UGC

Ya bayyana cewa a yanzu dai gwamnatin tarayya ta gabatar da bukatarta, inda ita ASUU ta jaddada cewa ya zama wajibi a kammala yarjejeniyar a rubuce, tare da matakan da kuma hukuncin da za a dauka, maimaikon yadda ake kulle yarjejeniyar a baki kawai tun bayan fara yajin aikin kungiyar a watanni biyu da suka gabata.

Idan za a iya tunawa, wannan taro na baya bayan nan, shine taronsu na bakwai wanda suka gudanar akan banbance banbancen da ake samu a tsakaninsu, wanda kuma kusan ana tashi taron ne ba tare da cimma wata matsaya ba.

Da yake kara jawabi, Farfesa Ogunyemi ya ce: "A jiya (Talata) ne gwamnatin tarayya ta gabatar da natabukatar garemu ba tare da jira amsa daga wajenmu ba, suka yi gaban kansu suka sanar cewa wai mun cimma matsaya. ASUU bata gudanar da aikinta a haka."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel