'Yan sanda sun tarwatsa magoya bayan PDP da barkonon tsohuwa a Jigawa

'Yan sanda sun tarwatsa magoya bayan PDP da barkonon tsohuwa a Jigawa

'Yan sanda sun badawa 'yan jam'iyyar PDP a jihar Jigawa barkonon tsohuwa kuma suka tarwatsa su a yayin da suka hallarci taron kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar na yankin Arewa maso yamma a garin Gumel.

The Nation ta ruwaito cewa 'yan sandan sun jefa barkonon tsohuwa ga dubban magoya bayan jam'iyyar ta PDP da suka fara taruwa a filin da za a kaddamar da yakin neman zaben.

"Hakan yasa mutanen suka fusata suka fara rera wakokin adawa da jam'iyyar APC da Buhari inda suke ihu suna cewa "Canji dole", "sai mun canja su".

Har ila yau: 'Yan sanda sun tarwatsa magoya bayan PDP da barkonon tsohuwa a Jigawa

Har ila yau: 'Yan sanda sun tarwatsa magoya bayan PDP da barkonon tsohuwa a Jigawa
Source: Twitter

Mataimakin Ciyaman din jam'iyyar, Alhaji Babandi Ibrahim ya shaidawa 'yan sanda cewa bai san abinda ke faruwa ba kwatsam sai dai suka ga 'yan sanda sun mamaye su.

DUBA WANNAN: An dakatar da sarakuna biyu a Zamfara saboda alaka da 'yan bindiga

"Mun nemi izinin yin taron kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar mu na Arewa maso yamma yau a Gumel amma kwatsam sai muka ka daruruwan 'yan sanda sun iso wajen taron suna korar mu," inji shi.

A bangarensu, hukumar 'yan sanda na jihar ta ce ba a tauyewa kowa haki ba, an basu shawarar dage taron ne ko kuma su canja wuri saboda ranar taron ya yi dai-dai da ranar da ake cin kasuwar garin kuma hakan zai haifar da cinkoso da yiwuwar afkuwar rikici.

"Ba hana su taro akayi ba, an bukaci su canja ranar taron ne saboda kasancewar ranar taron ya fado ranar kasuwar garin kuma bata gari na iya amfani da wannan damar domin tayar da hankulan jama'a," a cewar kwamishinan 'yan sandan jihar, Mr Bala Senchi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel