Buhari ya kaddamar da kwamitin shawara kan mafi karancin albashi

Buhari ya kaddamar da kwamitin shawara kan mafi karancin albashi

- Shugaba Buhari ya kaddamar da kwamitin shawara akan tsarin biyan sabon mafi karacin albashi ya kuma jadadda jajircewarsa wajen ganin an biya hakan

- Aikin da kwamitin za tayi shine duba tsarin biyan mafi karancin albashin ba tare da an samu Karin ciwo bashi ba

- Kwamitin da aka kaddamar zai kasance karkashin jagorancin kwararre a fanin kudi da tattalin arziki, Mista Bismarck Rewane

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 9 ga watan Janairu ya kaddamar da kwamitin shawara akan tsarin biyan sabon mafi karacin albashi sannan kuma ya jadadda jajircewarsa wajen ganin an biya hakan.

Da yake kaddamar da kwamitin jim kadan bayan zaman mako na bangaren zartarwa, Buhari ya sake bayyana jajircewasa waje sake duba mafi karancin albashi “domin lokacin yin hakan ne yanzu”.

A ranar 19 ga watan Disamba 2019, shugaban kasar yayinda yake gabatar da kasafin kudin 2019 ya sanar da kudirinsa na kafa kwamiti. Sannan ya ce za su yi duba ga dacewar hakan tare da tabbatar da hakan bai zamo dalilin karin ciwo bashi ba.

Buhari ya kaddamar da kwamitin shawara kan mafi karancin albashi

Buhari ya kaddamar da kwamitin shawara kan mafi karancin albashi
Source: Facebook

Buhari yace, "ya zama wajibi na bayyana maku cewa duk da karin mafi karancin albashin yana cikin jadawalin majalisar tarayya, muna kan gudanar da taro da gwammnonin jihohi don ganin cewa gwamnatin tarayya ta hada kai da su wajen ganin cewa an karawa ma'aikata albashin.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 9 da Buhari ya fada gaban kwamitin shawara kan albashi mafi karanci

Shugaban kasar ya kara da cewa kwamitin da ya kaddamar zai kasance karkashin jagorancin kwararre a fanin kudi da tattalin arziki, Mista Bismarck Rewane.

Sauran mambobin kwamitin sun kasance masu ilimi kan tattalin arziki da sha'anin mulki daga bagaren masu zaman kansu, wadanda ke aiki da sauran sassan gwamnati masu alaka.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel