Cikin shekaru 3: Yan Nigeria 104 suka mutu a wajen aikin Hajji - NBS

Cikin shekaru 3: Yan Nigeria 104 suka mutu a wajen aikin Hajji - NBS

Rahotannin da Legit.ng ta samu daga hukumar kididdiga ta kasa NBS, na nuni da cewa akalla 'yan Nigeria Musulmai 104 ne suka mutu a yayin gudanar daaikin Hajji a Saudiya, a cikin shekaru uku, yayin da daruruwa suka bace a yayin gudanar da aikin hajjin.

Wani rahoto na shekarar 2017 da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta saki, ya nuna cewa mahajjatan Nigeria 25 ne suka rasu a kasa mai tsarki a shekarar 2013, yayin da 33 suka rasu a 2014, sai 46 a shekarar 2015.

Hukumar NBS ta bayyana cewa ta samu wannan bayanin ne daga hukumar aikin Hajji ta Nigeria (NAHCON).

Rahoton ya kuma bayyana adadin yawan Musulmai mahajjata da suka bace daga shekarar 2014 zuwa 2016.

KARANTA WANNAN: Abubuwa 9 da Buhari ya fada gaban kwamitin shawara kan albashi mafi karanci

Cikin shekaru 3: Yan Nigeria 104 suka mutu a wajen aikin Hajji - NBS

Cikin shekaru 3: Yan Nigeria 104 suka mutu a wajen aikin Hajji - NBS
Source: Depositphotos

Binciken da ke kunshe a cikin rahoton ya yi nuni da cewa, a cikin shekarar 2014, mahajjata daya a kowacce jiha ta Zamfara da Nasarawa ne suka bace.

Duk da cewa babu wani rahoto kan bacewar mahajjata a shekarar 2015, duk da cewa an samu adadin mahajjata 78 a shekarar 2016.

Jihar Yobe ta samu adadin mahajjata 28 da suka bace a aikin hajji na shekarar 2016, yayin da jihohin Abia, Gombe da Sokoto suka samu karancin wadanda suka bace, da mutane daya kowacce jiha.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel