Yayinda yankin Arewa maso yamma tafi yawan kuri’u, Yankin Inyamurai ce mafi karancin kuri'u a 2019 – Rahoton INEC

Yayinda yankin Arewa maso yamma tafi yawan kuri’u, Yankin Inyamurai ce mafi karancin kuri'u a 2019 – Rahoton INEC

A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta gabatar da jimilla ta adadin al'ummar kasar nan da suka shiryawa babban zabe na 2019. Hukumar ta ce 'yan Najeriya 84,004,084 ke da rajista ta cancantar kada kuri'u a zaben.

Rahoton hukumar ya bayyana yawan mutanen da ake kyautata zaton zasu kada kuri’a a zaben da za’a gabatar a wata Febrairu da Maris na wannan shekara.

Jawabin ya nuna cewa yankin Arewa maso yammacin Najeriya ce tafi yawan kuri’u sannan yankin Yarbawa, kudu maso yamma.

KU KARANTA: Jihohi uku da duk wanda ya lashe kuri’unsu, ya lashe zaben 2019

Karanta jerin yankunan, adadin kurinsu, da jihohin da ke karkashinsu:

1. Arewa maso yamma : JIhar Kaduna, Kano, Jigawa, Kebbi, Zamfara, Sokoto da Katsina. Adadinsu 20,158,100

2. Kudu maso yammaci: Jihar Legas, Ogun, Ondo, Oyo, Osun, Ekiti. Adadinsu 16,292,212

3. Arewa maso tsakiya: Jihar Benue, Plateau, Nasarawa, Neja, Kwara da Abuja. Adadinsu 13,366,070

4. Kudu maso kudu: Jihar Cross River, Ribas, Delta, Edo, da Bayelsa. Adadinsu 12,841,279

5. Arewa maso yamma: Jihar Bauchi, Gombe, Taraba, Adamawa, Borno da Yobe. Adadinsu 11,289,293

6. Kudu maso yamma: Jihar Imo, Ebonyi, Anambara, Enugu da Abiya. Adadinsu 10, 057,130

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel