Tsoron hukunci ne ya sa Gamawa guduwa APC – Yakassai

Tsoron hukunci ne ya sa Gamawa guduwa APC – Yakassai

An alakanta sauya shekar mataimakin shugaban jam’iyyar People’s Democratic party (PDP), Babayo Gamawa zuwa All Progressive Congress (APC), tare da wani jigo a kwamitin amintattu na jam’iyyar Kaulaha Aliyu, da guje ma hukunci.

Ana dai zargin jam’iyya mai mulki da farautar yan siyasa daga jam’iyyun adawa inda take hukuntasu.

Jigon arewa Tanko Yakasai ya bayyana cewa Gamawa na tsoron fuskantar hukunci ne shiyasa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Tsoron hukunci ne ya sa Garmawa guduwa APC – Yakassai

Tsoron hukunci ne ya sa Garmawa guduwa APC – Yakassai
Source: Facebook

Yakasai ya fadi haka e yayinda yake martani ga sauya shekar Gamarya zuwa jam’iyya mai mulki da kuma ganawar da yayi da shugaban Kasa Muhhammadu Buhari a daren jiya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

“Ina iya baku tabbacin cewa a kullun jam’iyya mai mulki na farautarsu ta hanyar amfani da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma rundunar yan sandan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 9 da Buhari ya fada gaban kwamitin shawara kan albashi mafi karanci

“Amma shawara ta ga wadannan yan siyasan sine cewa su daina jin tsoro saboda komai zai zama labari nan bada jimawa ba,” inji shi.

Ya caccaki tsalon yaki da rashawar shugaban kasa wacce ke ba barayin yan siyasa kariya idan suka yarda suka koma APC amma sai ayi ta tozarci da razana wadanda suke jam’iyyun adawa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel