Yanzu Yanzu: Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Gombe ya koma PDP

Yanzu Yanzu: Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Gombe ya koma PDP

- Mukaddashin shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Gombe, Honourable Maigari Jungudo, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

- Ya zargi tsohuwar jam’iyyarsa da rashin adalci ga wasu mambobin j am’iyyar da aka asassa APC da su a jihar

- Sauya shekar nasa na zuwa ne yan watanni kadan bayan mambobin majalisar dokokin ihar biyu sun bar APC zuwa PDP wacce dama it ace mai rinjaye a majalisar dokokin jihar

Mukaddashin shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Gombe, Honourable Maigari Jungudo, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Dan majalisar mai wakiltan Funakaye ta arewa yayinda yake sanar da sauya shekar nasa ya zargi tsohuwar jam’iyyarsa da rashin adalci ga wasu mambobin jam’iyyar da aka asassa APC da su a jihar.

Yanzu Yanzu: Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Gombe ya koma PDP

Yanzu Yanzu: Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Gombe ya koma PDP
Source: Depositphotos

Sauya shekar nasa na zuwa ne yan watanni kadan bayan mambobin majalisar dokokin ihar biyu sun bar APC zuwa PDP wacce dama it ace mai rinjaye a majalisar dokokin jihar.

Daga baya sai yan majalisar suka gabatar da dokar tsare-tsare na 2019 na kananan hukumomi goma sha daya a Gombe, inda aka aiwatar da ita a doka.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na bar PDP – Tsohon mataimakin shugaban jam’yyar na kasa

A wani lamari makamancin haka, mun ji cewa Sakataren jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Sakaba ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tare da dimbin magoya bayansa.

Sakaba, wanda gwamnan jihar Atiku Bagudu ya tarba ya sanar da ficewars daga PDP ne a ranar Laraba a Birnin Kebbi kamar yadda muka samu daga Daily Trust.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel