Abubuwa 9 da Buhari ya fada gaban kwamitin shawara kan albashi mafi karanci

Abubuwa 9 da Buhari ya fada gaban kwamitin shawara kan albashi mafi karanci

A ranar Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin shawara kan kaddamar da sabon tsarin lbashi mafi karanci ga ma'aikatan kasar, inda ya tabbatar da kudurinsa na ganin cewa an fara biyan sabon albashin ba tare da bata lokaci ba.

A lokacin da yake kaddamar da kwamitin jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa (FEC), Buhari ya kara jaddada aniyarsa na sake fasalin tsarin abashi mafi karancin tare da zatbare wani kaso daga ciki, kasancewar lokacin hakan ya yi.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Buhari zai zabtare albashin masu daukar sama da mafi karancin albashi

Abubuwa 9 da Buhari ya fada gaban kwamitin shawara kan albashi mafi karanci

Abubuwa 9 da Buhari ya fada gaban kwamitin shawara kan albashi mafi karanci
Source: Depositphotos

Ga muhimman bayanai 10 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a wajen taron kaddamar da kwamitin.

1. A shekarar 2011 aka sabunta albashi mafi karanci a Nigeria. Wanna ya nuna cewa ya zama wajibi a sake sabunta shi, duk da cewa akwai matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta. Wannan ne dalilin da ya sa na kafa kwamitin da zai duba yiyuwar sabunta albashi, inda aka tattauna da kungiyoyin kwadago, tare da gabatarwa gwamnati rahoto kan kara albashi mafi karanci ga ma'aikatan kasar.

2. Kwamitin ya gabatar da rahotonsa tare da wasu bukatu da yake ganin ya kamata a cika su. Zuwa yanzu muna kan nazarin wadannan bukatu da kuma daukar matakin karshe wanda zai kaiga gabatar da kudurin dokar sabunta albashin gaban majalisar zartsawa.

3. Ina so kowa ya sani cewa babu wata alamar tambaya akan wai ko za a kara albashi mafi karanci daga N18,000 zuwa wani mizani na gba. Ina baku tabbacin cewa zan tabbata an kara albashin.

4. Haka zalika, ya zama wajibi na bayyana maku cewa duk da karin mafi karancin albashin yana cikin jadawalin majalisar tarayya, muna kan gudanar da taro da gwammnonin jihohi don ganin cewa gwamnatin tarayya ta tafi kafada-da-kafada da su wajen ganin cewa an karawa ma'aikata albashin.

5. Wanna kuwa ya zama wajibi la'akari da matsaloli da nakasun da ake samu wajen shigar kudaden haraji, wanda ya sa hakan yayi matukar wahala ga wasu gwamnonin su rika biyan ma'aikatan jiharsu akan lokaci.

6. Kamar yadda kuka sani, a matakin gwamnatin tarayya, mun aiwatar da duk wasu abubuwan da ya kamata na ganin cewa mun kara albashi mafi karancin, inda har muka sanya shi a cikin kasafin kudn 2019, wanda tuni muka gabatarwa majalisar tarayya. Don haka, zamu iya samun damar cimma kudirinmu na sake fasalin kudin ma'aikatan da ke daukar sama da mafi karancin albashi a kasar.

7. Sai dai, muna da kudurin ganin cewa bayan an tabbatar da wucewar kudurin dokar sabunta mafi karancin albashin, to zamu kuma duba yiyuwar zabtare wani kaso daga cikin albashin ma'aikatan da dama tuni suna daukar sama da mafi karancin albashin, don ganin cewa an samu dai-daito a wajen cimma wannan kuduri na sabunta albashin.

8. Bisa wannan dalilin ne yasa na kafa kwamitin da zai rinka baiwa gwanati shawara kan hanyoyin da za a samar da kudaden kaddamar da sabon albashi mafi karanci, ta hanyar da zai dore, karin kudin zai kara yawan kasafin albashin da ake aikawa ma'aikata, wanda ya samuke da kudirin zabtare wani kaso daga cikin albashi wadanda dama tuni can suna daukar sama da mafi karancin albashin.

9. Kwamitin da na kaddamar yau zai kasance karkashin jagorancin kwararre a fanin kudi da tattalin arziki, Mr. Bismarck Rewane. Sauran mambobin kwamitin sun kasance masu ilimi kan tattalin arziki da sha'anin mulki daga bagaren masu zaman kansu, wadanda ke aiki da sauran sassan gwamnati masu alaka.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel