Zaben 2019 zai zama haramiyar gwamnati idan ba ta tabbatar da mafi karancin albashin ma'aikata ba - Kungiyar Kwadago

Zaben 2019 zai zama haramiyar gwamnati idan ba ta tabbatar da mafi karancin albashin ma'aikata ba - Kungiyar Kwadago

- Kungiyar kwadago ta ce za ta kauracewa zaben 2019 muddin gwamnati ba ta tabbatar da mafi karancin albashin ma'aikata ba na N30,000 cikin dokar kasa

- Kungiyar reshen jihar Anambra da Imo ta bai wa gwamnati wa'adin kwanaki bakwai ko kuma kilu ta ja bau

- Ana neman shugaban kasa Buhari da kuma gwamnonin Najeriya kan tabbatar da wannan kudiri gabanin zaben 2019

Kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Imo, a jiya Talata ta sake gargadin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya gaggauta tabbatar da mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan na N30,000 ko kuma kilu ta janyo ma sa bau.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, kungiyar ta gargadi shugaban kasa Buhari da ya gaggauta tabbatar da mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan domin kuwa hakan na iya janyo barazana ta haramci da kauracewa zaben 2019.

Kazalika reshen kungiyar na jihar Anambra, ya sha alwashin rashin goyon bayan kowace jam'iyyar siyasa a yayin babban zaben kasa muddin gwamnati ta gaza tabbatar da sabon mafi karancin albashin ma'aikata.

Zaben 2019 zai zama haramiyar gwamnati idan ba ta tabbatar da mafi karancin albashin ma'aikata ba - Kungiyar Kwadago

Zaben 2019 zai zama haramiyar gwamnati idan ba ta tabbatar da mafi karancin albashin ma'aikata ba - Kungiyar Kwadago
Source: Depositphotos

Kungiyar kwadago reshen jihohin biyu da suka yi tarayyar wannan kira sun bayyana hakan ne yayin zanga-zangar lumana da suka gudanar a rassan su kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Ko shakka ba bu ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin kungiyar kwadago, gwamnatin tarayya da kuma gwamnonin kasar nan dangane da dambarwa ta tabbatar da Naira 30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikata.

Kungiyar ta bayar da wa'adin kwanaki bakwai ga gwamnatocin Najeriya wajen tabbatar da wannan babban kudiri da ta shafe tsawon lokuta ta na ci gaba da muradi domin inganta jin dadin ma'aikata a fadin kasar nan ko kuma kilu ta ja bau.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da cibiyar sadarwar zamani

Bugu da kari, kungiyar ta lashi takobin juya baya ga shugaban kasa ko wani gwamna da ya hau kujerar naki ta tabbatar da kudirin mafi karancin albashi cikin dokar kasa a yayin babban zaben kasa ya gabato.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari na ci gaba da kirdadon kwamitin da ya kafa domin aiwatar da bincike kan tabbatar da sabon mafi karancin albashin ma'aikata ba tare da kawo nakasu ga tattalin arziki ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel