2019: Wani babban basaraken arewa ya yi barazanar tsinewa 'yan siyasa

2019: Wani babban basaraken arewa ya yi barazanar tsinewa 'yan siyasa

- Sarkin Tiv, Farfesa James Ayatse ya yi kira ga 'yan siyasar jihar Benue su guyi tayar da tarzoma a yanzu da ake fuskantar zaben 2019

- Basaraken ya yi barazanar cewa duk wani da ya yi yunkurin tayar da hankulan al'umma ya kuka da kansa bisa abinda zai biyo baya

- Ayatse ya yi wannan gargadin ne a taron saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan takarar gwamna 32 suka hallarta a jihar

Sarkin al'ummar Tiv kuma Shugaban kwamitin sarautun gargajiya na jihar Benue, Tor Tiv, Farfesa James Ayatse ya yi kira ga 'yan siyasa su guji tayar da tarzoma da daukan nauyin 'yan bangan siyasa idan kuma ba haka ba tsinuwa zata fadawa kasar.

Basaraken ya yi barazanar cewa duk wani dan siyasa da ke da niyyar tayar da rikici a jihar a yayin zabe ko bayan zabe ya shiryawa sakamakon da zai biyo baya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

2019: Wani babban basaraken arewa ya yi barazanar tsinewa 'yan siyasa

2019: Wani babban basaraken arewa ya yi barazanar tsinewa 'yan siyasa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Boko Haram sun sake tafka wani sabon ta'addanci a Borno

"A kullum sarakunan gargajiya zaman lafiya suke kokarin jadadawa soboda su abin yafi shafa idan ana rikici. Duk wanda ke son tayar da rikici, zai hadu da hukuncin da ya dace da shi. Dole mu dena tayar da tarzoma.

"Saboda haka ina kira ga 'yan siyasa su guji tayar da tarzoma," inji shi.

Ayatse ya yi wannan jawabin ne a yayin saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan takarar gwamna 32 daga jam'iyyu daban-daban suka rattaba hannu a kai. Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ne ta shirya taron.

"Masu sarautun gargajiya ne ke zaune tare da al'umma kuma sun san wahalhalun da mutane ke ciki. Mun san wahalhalun da muka shiga a lokacin da rikici ya barke a jihar Benue. Mu zaman lafiya muke so kuma za muyi duk mai yiwuwa domin tabbatar da hakan." a cewar Ayatse.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel