Tayar da tarzoma: 'Yan sanda sun shiga neman shugaban NURTW na Legas ruwa a jallo

Tayar da tarzoma: 'Yan sanda sun shiga neman shugaban NURTW na Legas ruwa a jallo

Rundunar 'yan sanda ta bayar da cigiyar wani jigo a NURTW, Mustapha Adeleke (Seigo) ruwa a jallo bisa zarginsa da tayar da tarzoma a wurin taron kaddamar da kamfen din APC a jihar Legas a jiya Talata. Seigo da tawagarsa sun farma wani jigo a NURTW din ne mai suna MC Oluomo inda suka yi masa rauni tare da hargitsa taron.

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta damke mutane biyu kuma tana neman wani shugaba na kungiyar direbobin kasa NURTW, Mustapha Adekunle wanda akafi sani da Seigo ruwa a jallo saboda tayar da tarzoma da su kayi yayin kaddamar da yakin neman zaben APC a ranar Talata a Legas.

Kazamin rikici ya barke a wurin taron kaddamar da yakin neman zaben na APC a jiya Talata inda wasu mutane da dama suka jikkata sakamakon fada ta ya barke tsakanin bangarori biyu na kungiyar NURTW.

Tayar da tarzoma: 'Yan sanda sun shiga neman shugaban NURTW na Legas ruwa a jallo

Tayar da tarzoma: 'Yan sanda sun shiga neman shugaban NURTW na Legas ruwa a jallo
Source: Depositphotos

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Legas, Chike Oti ya ce mutanen biyun da aka kama suna taimakawa 'yan sanda wurin cigaba da binciken musababbin tayar da tarzomar a cikin sanarwar da ya fitar.

DUBA WANNAN: Boko Haram sun sake tafka wani sabon ta'addanci a Borno

Mr Oti ya ce Siego da tawagarsa sun shigo wurin kaddamar da yakin zaben ne a matsayinsu na magoya bayan jam'iyya amma kwatsam sai 'yan tawagarsa suka kaiwa wani shugaban na NURTW mai suna MC Oluomo hari.

"Shugaba a NURTW, Mustapha Adekunle da akafi sani da Seigo ya iso wurin taron da tawagarsa a matsayin magoya bayan jam'iyyar.

"Amma daga bisani sai Seigo da tawagarsa suka fadawa wasu magoya bayan jam'iyyar da fada.

"Sakamakon rikicin a yiwa wani jigo a NURTW, MC Oluoma rauni inda aka garzaya dashi asibitin Eko yayin da wasu mutane biyu suma sun jikkata kuma sun asibitin koyarwa na jami'ar Legas suna karbar magani.

"Yan sanda sunyi gagawar kawo karshen rikicin a wurin taron," inji sanarwar.

"Da haka ne rundunar 'yan sanda ke kra da al'umma su taimaka mata da duk wani bayani da zai taimaka a gano inda Mustapha Adekunle wanda akafi sani da Seigo ya ke a halin yanzu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel