Yanzu Yanzu: Wata ministar Buhari ta sake yin murabus

Yanzu Yanzu: Wata ministar Buhari ta sake yin murabus

- Khadija Bukar Abba Ibrahim, ta yi murabus daga matsayinta na minista

- Karamar ministar harkokin wajn ta sauka daga matsayinta ne domin samun damar neman takara a zaben 2019.

- Tana neman takarar kujerar yar majalisa mai wakiltan mazabar Damaturu/Tarmuwa/Gujba/ da ke jihar Yobe a majalisar dokokin kasar

Karamar ministar harkokin waje, Khadija Bukar Abba Ibrahim, ta yi murabus daga matsayinta domin samun damar neman takara a zaben 2019.

Tana neman takarar kujerar yar majalisa mai wakiltan mazabar Damaturu/Tarmuwa/Gujba/ da ke jihar Yobe a majalisar dokokin kasar.

Yanzu Yanzu: Wata ministar Buhari ta sake yin murabus

Yanzu Yanzu: Wata ministar Buhari ta sake yin murabus
Source: Facebook

Ta kayar da danta, Mohammed Bukar Abba inda ta zamo yar takarar majalisar wakilai mai wakiltan yankin Damaturu/Tarmuwa/Gujba/Gulani da ke jihar Yobe a zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka yi watan Oktoban shekarar da ya gabata.

Ta samu kuri’u 1,295 yayinda dan mijinta ya samu kuri’u 15.

Hajiya Khadija wacce aka ba mukamin minister a 2015, ce minister ta shida da suka yi murabus daga majalisar shugaban kasar.

Ta tabbatar wa wasu manema labarai a fadar shugaban kasa cewa taron yan majalisa da ake duk ranar Laraba na wannan makon shine na karshe da za ta halarta, jim kadan kafin fara taron.

KU KARANTA KUMA: Ekweremadu da gwamnonin PDP na kudu maso gabas na yiwa Buhari aiki – BMO

A wani lamari na daban, mun ji cewa Rotimi Amaechi, Darakta Janar na kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta iya doke jam’iyya mai mulki ne a wajen rashawa kawai.

Ya bayyana hakan yayinda yake jawabi a wajen babban gangamin da aka gudanar a jihar Adamawa a ranar Talata, 8 ga watan Janaru, inda ya kalubalanci PDP da ta nuna shirin da tayi wa yan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel