Dalilin da yasa na bar PDP – Tsohon mataimakin shugaban jam’yyar na kasa

Dalilin da yasa na bar PDP – Tsohon mataimakin shugaban jam’yyar na kasa

- Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Babayo Gamawa, yayi bayanin dalilin da yasa ya bar jam’iyyar zuwa APC

- Ya zargi shugabanin babbar jam’iyyar adawar kasar da dakatar da shi ba tare da an ji ta bakinshi ba

- A ranar Talata, 8 ga watan Janairu ne uwar jam’iyya ta dakatar da Gamawo kan zargin watsar da ayyukansa da kuma aikata abubuwan da suka sabama jam’iyyar

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Sanata Babayo Gamawa, yayi bayanin dalilin da yasa ya bar jam’iyyar sannan ya koma jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Ya zargi shugabanin babbar jam’iyyar adawar kasar da dakatar da shi ba tare da an ji ta bakinshi ba.

Dalilin da yasa na bar PDP – Tsohon mataimakin shugaban jam’yyar na kasa

Dalilin da yasa na bar PDP – Tsohon mataimakin shugaban jam’yyar na kasa
Source: Facebook

“Kawai zargi ne ba tare da anji ta bakin bangare daya ba, sun bayyana cewa sun dakatar dani daga mukamina. Ina so nayi kira a gare su da su duba sakatariya. A siyasa, ya kamata su san abubuwan da ke faruwa a sakatariyar a kullun,” inji shi.

Furucinsa na zuwa jim kadan bayan wata ganawa tare da shuaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

KU KARANTA KUMA: Ekweremadu da gwamnonin PDP na kudu maso gabas na yiwa Buhari aiki – BMO

A ranar Talata, 8 ga watan Janairu ne uwar jam’iyya ta dakatar da Gamawo kan zargin watsar da ayyukansa da kuma aikata abubuwan da suka sabama jam’iyyar.

Da yake martani akan dakatar dashi, yace shugaban am’iyyar za zai yi danasanin matakin da ya dauka akan shi domin ko kadan shi abun bai dameshi ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel