Ba shiga ba fita: Dakarun Sojin Najeriya sun tare wata babbar hanya a Arewa maso gabas

Ba shiga ba fita: Dakarun Sojin Najeriya sun tare wata babbar hanya a Arewa maso gabas

Dakarun rundunar Sojan kasa ta Najeriya sun rufe babbar hanyar da ta tashi daga garin Maiduguri zuwa Damaturu zuwa garin Potiskum na jahar Yobe, a wani dabara na yaki da yayan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito baya ga rufe hanyar, an hangi Sojoji suna ta faman safa da marwa akan motocin yaki tare da gudanar da sintiri dauke da makamai akan titin, kamar yadda sakataren yan Yuniyon NURTW, Malam Nusu ya bayyana.

KU KARANTA: Buhari ya bayyana abinda yasa bai tsige Buratai, Saddique da sufetan Yansanda ba

Sai dai Malam Nuhu yace bashi da takamaimen masaniya kan dalilin da yasa Sojoji suka rufe hanyar, amma yace yana tunanin hakan baya rasa nasaba da hare haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a yan kwanakin nan.

“Hanyar bata biyuwa cikin sauki tun daga watan Disambar bara zuwa yanzu, kowa na kuka da hanyar daga direbobi har fasinjoji, ga tsawonta yah aura kilomita dari biyu, kowa addu’a kawai yake yi akan wannan hanyar.

“Bamu san manufarsu ta riude hanyar ba, amma idan manufar itace don zakulo masu tayar da kayar baya, toh muna maraba da ita, amma kamar yadda na fada, bata rasa nasaba da sabon yaki da yan ta’adda da Sojoji suka kaddamar.” Inji shi.

Haka zalika wani mazaunin garin Damaturu, babban birnin jahar Yobe ya shaida ma majiyarmu cewa sun samu labarin wani hari da yan Boko Haram suka kai a garin Ngamdu, harin da yace sun kwashe awanni suna cin karensu babu babbaka.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi don jin ta bakin hukumomin Soji da na Yansanda kan dalili rufe hanyar ya ci tura, sakamakon dukkansu sun bayyana cewa basu da wata masaniya game da hakan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel