Da dumi dumi: Yan bindiga da sun yi garkuwa da wata kansila Mace a Katsina

Da dumi dumi: Yan bindiga da sun yi garkuwa da wata kansila Mace a Katsina

Matsalar tsaro data dangancin ayyukan miyagu masu garkuwa da mutane ya cigaba da ta’azzara a jahar Katsina, inda wasu gungun yan bindiga suka yi awon gaba da wata mata mai rike da mukamin kansila a jahar Katsina.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Usaini Iliyasu Charanchi ne ya bayyana haka a shafinsa, inda yace wannan lamari ya faru ne a daren Laraba, 9 ga watan Janairu, da misalin karfe 1:30.

KU KARANTA; Sha’awa ta jefa wani mutum ga matsala bayan ya zakke ma matar makwabcinsa a Katsina

Da dumi dumi: Yan bindiga da sun yi garkuwa da wata kansila Mace a Katsina

Amina
Source: Facebook

Majiyar Legit.com ta ruwaito yar siyasar wanda sunanta Amina Bello Maje, itace kansila mai wakiltar amzabar Majan Wayya a majalisar shugabanci ta karamar hukumar Charanchi ta jahar Katsina.

Bugu da kari majiyar ta bayyana cewa mahaifin kansila Amina, Alhaji Bello Maje, shine tsohon dan majalisa dake wakiltar karamar hukumar Charanchi a majalisar dokokin jahar Katsina.

A wani labarin kuma, Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana damuwarsa da yadda yan fashi da makami, yan bindiga dadi da kuma miyagu masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka a fadin jahar Katsina.

Legit.com ta ruwaito Masari ya bayyana haka ne a ranar Laraba 2 ga watan Janairu, yayin daya bude taro na musamman na majalisar tsaro ta jahar Katsina don tattauna batutuwan da suka danganci matsalolin tsaro a jahar, tare da hanyoyin magancesu.

Bugu da kari gwamnan ya bayyana yadda wasu barayi suka yi tsinke ma fadar gwamnatin jahar Katsina dake GRA, inda suka sace wasu kayan wuta dake kusa da fadar gwamnatin, a cewarsa hakan ya nuna tsananin tabarbarewar tsaro a jahar.

Daga karshe Masari yayi kira da dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro dasu tattauna don lalubo hanyoyin magance rikicin, inda ya kara da cewa kada su boye bayanin da suke da shi akan wasu miyagun mutane, domin ta haka ne kadai jami’an tsaro zasu kamasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

S

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel