Lagas-Ibadan: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin shigo da jiragen kasa 30 da taragu 300

Lagas-Ibadan: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin shigo da jiragen kasa 30 da taragu 300

- Gwamnatin tarayya ta yi umurnin shigo da jiragen kasa 30 da kuma tagu 300 zuwa tashar jirgin kasa na Lagas-Ibadan idan aka kammala aikin

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, yace jiragen da taragun za su habbaka tsarin zirge-zirga na fasinjoji da kayayyaki daga Lagas zuwa wasu wuraren a kudu maso yamma

Gwamnatin tarayya ta yi umurnin shigo da jiragen kasa 30 da kuma tagu 300 zuwa tashar jirgin kasa na Lagas-Ibadan idan aka kammala aikin.

A cewar ministan sufuri, Rotimi Amaechi, jiragen da taragun za su habbaka tsarin zirge-zirga na fasinjoji da kayayyaki daga Lagas zuwa wasu wuraren a kudu maso yamma.

Lagas-Ibadan: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin shigo da jiragen kasa 30 da taragu 300

Lagas-Ibadan: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin shigo da jiragen kasa 30 da taragu 300
Source: UGC

“Muna sanya ran iragen kasa 30 da taragu 300,” Amaechi ya bayyana hakan yayinda yaje jawabi a wani ziyarar gani da ido da ya kai wajen da ayyuka ke gudana wanda kamfanin China Civil Engineering Construction Company kee gudanarwa.

A nashi bangaren, Manajan Darakta na hukumar jiragen kasa na Najeriya Fidet Okhiria, yace hukumar na tsimayin wasu kayayyaki biyu kowannensu dauke da jirage 10.

KU KARANTA KUMA: A fannin rashawa kadai ne PDP za ta iya doke mu – Amaechi

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta bayar da umurni ga masu ginin tashar jirgin Lagas-Ibadan da su kammala aikin Iju (Lagas) zuwa Agbado (Ogun) cikin makonni biyu.

A cewar gwamnatin koda da dukkanin ayyukan na da muhimmanci akwai bukatar kammala wannan saboda yawan zirga-zirgan da ake yi a hanyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel