A fannin rashawa kadai ne PDP za ta iya doke mu – Amaechi

A fannin rashawa kadai ne PDP za ta iya doke mu – Amaechi

- Darakta Janar na kungiyar kamfen din Buhari, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta iya doke jam’iyya mai mulki ne a wajen rashawa kawai

- Rotimi ya kalubalanci PDP da ta nuna shirin da tayi wa yan Najeriya

- Ya kuma zargi PDP da hargagi don kara samun shugabancin kasar domin ta sake satar wasu kudaden sannan ta dawo da kudaden da tayi amfani da shi a lokacin zabe

Rotimi Amaechi, Darakta Janar na kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta iya doke jam’iyya mai mulki ne a wajen rashawa kawai.

Ya bayyana hakan yayinda yake jawabi a wajen babban gangamin da aka gudanar a jihar Adamawa a ranar Talata, 8 ga watan Janaru, inda ya kalubalanci PDP da ta nuna shirin da tayi wa yan Najeriya.

A fannin rashawa kadai ne PDP za ta iya doke mu – Amaechi

A fannin rashawa kadai ne PDP za ta iya doke mu – Amaechi
Source: UGC

“Wannan zaben tsakanin jam’iyyu biyu da suka yi mulki ne. Muna kalubalantar PDP da ta bude wani muhawara inda jama’a za su hallara. Sai su nuna mana sakamakonsu sannan muma mu nuna namu. Wajen da za ta doke mu kawai shine a rashawa,” inji shi.

Amaechi ya kuma zargi PDP da hargagi don kara samun shugabancin kasar domin ta sake satar wasu kudaden sannan ta dawo da kudaden da tayi amfani da shi a lokacin zabe.

KU KARANTA KUMA: Watsa min acid ya kara min kwarin gwiwa ne – Nura M Inuwa

A wani labari na daban mun samu labari dazu cewa bankin nan na Najeriya da aka saida kwanaki ya fito ya raba gardama game da zargin da ake yi na cewa shugaban kasa Buhari yana cikin wadanda su ka zuba masa jari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel