Sayen katin zabe asarar kudi da bata lokaci ne - INEC

Sayen katin zabe asarar kudi da bata lokaci ne - INEC

- A kwanakin baya ne wani kwamishinan a hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ya bayyana cewar zasu duba yiwuwar sanar da sakamakon zabe kai tsaye ta na'ura

- Ana cigaba da musayar mabanbantan ra'ayi a kan nada Amina Zakari a matsayin shugabar tattara sakamakon zaben shugaban kasa

- INEC ta ce duk 'yan siyasar dake sayen katin zabe na asarar kudi da lokacinsu ne

A jiya, Talata, ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewar ba zata sanar da sakamakon zabukan 2019 kai tsaye ta na'ura ba kamar yadda wasu ke tsammanin zata yi ba.

A wani taro na masu ruwa da tsaki da hukumar tayi jiyan, Farfesa Mahmoud Yakubu, shugaban INEC, ya ce babu wata data tilasta wa hukumar sa yin hakan.

Kazalika INEC tayi shagube da gugar zana ga 'yan siyasar dake sayen katin zaben masu kada kuri'a, tana mai bayyana yin hakan da cewar bata lokaci ne da asarar kudi kawai domin hukumar ta wuce nan a shirye-shiryenta na magance magudin zabe.

Sayen katin zabe asarar kudi da bata lokaci ne - INEC

Farfesa Mahmoud Yakubu
Source: Depositphotos

Mahmoud ya ce, "sayen katin zabe daga hannun wasu masu kada kuri'a asara ce kawai. Wasu daga cikin masu sayen katin zaben na yin haka ne bisa tunanin zasu iya amfani da su ta haramtacciyar hanya a shafin mu na yanar gizo.

"Abin bakin ciki ne yadda wasu 'yan siyasa ke aiki tukuru don ganin sun samu damar yin amfani da haramtattun hanyoyi don kawo cikas a duk wani tsari da muke da shi wajen gudanar da sahihin zabe.

DUBA WANNANA: Na bar APC ne saboda Buhari ya ki amsa kira na - Na hannun damar shugaban kasa

Har yanzu hukumar INEC na cigaba da shan suka dangane da batun nada Amina Zakari a matsayin wacce zata jagoranci kwamitin tattara sakamakon zaben shugaban kasa. Masu sukar INEC na kafa hujja ne da cewar bai kamata ta bawa Amina wannan aiki ba saboda tana da alaka ta jini da shugaba Buhari.

Sai dai Amina ta musanta wannan zargi tare da bayyana cewar tsohon shugaban kasa Jonathan ne ya fara nada ta mukamin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel