Ruguza Tinubu a Kwara: Saraki ya roki masu kada kuri'a su yafewa yan takarar PDP

Ruguza Tinubu a Kwara: Saraki ya roki masu kada kuri'a su yafewa yan takarar PDP

- Sanata Bukola Saraki, ya ce babu wata hanya da Asiwaju Ahmed Tinubu zai samu damar samun hanyar shiga gidan gwamnatin jihar Kwara

- Saraki ya roki masu kada kuri'a da su yafewa 'yan takarar PDP da suka yi masu wani laifi, tare a bukatarsu akan zabar PDP don ci gaban jihar

- Yace jam'iyyar hamayya a jihar, APC, da 'yan takararta makiyan ci gaban jihar Kwara ne, wadanda ke son kai jihar zuwa Kudu maso Yamma

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya ce babu wata hanya da jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Ahmed Tinubu zai samu damar samun hanyar shiga gidan gwamnatin jihar Kwara, a lokaci daya kuma yana rokon masu kada kuri'a da su yafewa 'yan takarar PDP da suka yi masu wani laifi, tare a bukatarsu akan zabar PDP don ci gaban jihar.

Saraki ya bayyana hakan ne a yayin taron kaddamar da yakin zaben dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP, Hon Abdulrazaq Atunwa, da kuma sauran 'yan takara a kujeru daban daban na jam'iyyar a jihar, wanda ya gudana a Bode-Sadu, karamar hukumar Moro da ke jihar.

Ya ce: "Duk wani laifi da kuke tunanin wani dan takarar jam'iyyarmu yayi mau, ku yafe masa ko don saboda ni, da kuma kare martabar jihar Kwara, ina fatan zaku zabi jam'iyyar PDP daga sama har kasa a zabe mai zuwa. Kar ku damu, duk wanda ya gaza aiwatar da aiki da muka turashi, to tare zamu tsige su."

KARANTA WANNAN: Lauyoyi sun fafata a kotu kan takaddamar sanya hijabi a makarantun jihar Ogun

Ruguza Tinubu a Kwara: Saraki ya roki masu kada kuri'a su yafewa yan takarar PDP

Ruguza Tinubu a Kwara: Saraki ya roki masu kada kuri'a su yafewa yan takarar PDP
Source: UGC

Yace jam'iyyar hamayya a jihar, APC, da 'yan takararta makiyan ci gaban jihar Kwara ne, wadanda ke son kai jihar zuwa Kudu maso Yamma, don haka ya bukaci masu kada kuri'a dasu kaucewa jam'iyyar APC da 'yan takararta.

"Bari na tuna maku, kamar yadda suka yi watanni kadan kafin zaben 2015, haka suke yi a yanzu, suna manna fastoci da allunan tallarsu, suna son samun kujerar gwamnan jihar ta kowacce hanya. Wadannan sune dai mutanen da suka kasa kashe koda N100,000 ga al'ummar yankunansu. Kuma suna son kai Kwara zuwa Kudu maso Gabas, suna son yin amfani da farfaganda da karairayi, to ina fatan ba zaku biye masu ba.

"Mu dai mun san kanmu, munga yadda suka gaza cika alkawuran da suka daukar mana tsawon shekaru kusan hudu na gwamnatinsu. Don haka ya zama wajibi mu mayar da su gida, su tafi da yunwa, talauci da matsatsin rayuwar da suka jefa mutane ciki, uwa uba ga matsalar rashin tsaro.

"Ina mai tabbatar maku, duk wani yunkuri na Sanata Bola Tunubi da sauran 'yan kazaginsa ba zai yi tasiri wajen juya akalar jihar Kwara a zabe mai zuwa ba. Nan ba Kudu maso Gabas bane, nan jihar Arewa ce, babu wani wanda zaizo ya mayar da mu kamar wasu bayi da za a ja akalarsu yadda ake so."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel