Zaben 2019 ba game dani bane - Saraki

Zaben 2019 ba game dani bane - Saraki

- Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana cewa zaben 2019 a jihar Kwara akan kare al’ada mutanen jihar ne

- Saraki ya kuma kara da cewa ya zama dole mutanen jihar Kwara su lalata shirin da wasu yan siyasar a mutu ko ayi rai da yan barandarsu don mayar da jihar kudu maso yamma

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ta bayyana a jiya cewa zaben 2019 a jihar Kwara akan kare al’ada mutanen jihar ne.

Ya kara da cewa zaben ba akan shi game da shi bane a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa haka kuma ba game da dan takarar gwamna na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) bane.

Saraki ya kuma kara da cewa ya zama dole mutanen jihar Kwara su lalata shirin da wasu yan siyasar a mutu ko ayi rai da yan barandarsu don mayar da jihar kudu maso yamma.

Zaben 2019 ba game dani bane - Saraki

Zaben 2019 ba game dani bane - Saraki
Source: Depositphotos

Yace jihar Kwara na al’umman Kwara ne sannan duk wani kokari da yan siyasar bangarenci ke yi don mikawa masu mulki daga Lagas da Abuja yankin ba zai cimma nasara ba.

Shugaban majalisar dattawan yayi Magana ne a Bode Saadu, hedkwatar karamar hukumar Moro da ke arewacin Kwara a lokacin kaddamar da kamfen din PDP.

KU KARANTA KUMA: Watsa min acid ya kara min kwarin gwiwa ne – Nura M Inuwa

A wani lamari na daban, mun ji cewa kungiyar labaran shugaba Buhari wato Buhari Media Organisation (BMO) ta yaba ma abunda ta bayyana a matsayin mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta bayyana cewa hatta ga yan takarar Peoples Democratic Party (PDP) a arewacin Najeriya na kokarin ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress APC ya zarce.

Hakan na zuwa ne a lokacin da kungiyar tayi zargin cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da gwamnonin PDP a kudu maso gabas na yiwa shugaban kasar aiki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel