'Yan sandan Najeriya sun gaza sauke nauyin da rataya a wuyansa - Buhari

'Yan sandan Najeriya sun gaza sauke nauyin da rataya a wuyansa - Buhari

A yayin da hukumar 'yan sandan Najeriya ta daura damarar tare da shan alwashi na tabbatar da tsaro yayin babban zaben kasa na 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya fede ma ta biri har wutsiya da cewa ta gaza sauke nauyin da rataya a wuyanta.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sakamakon yadda hukumar 'yan sandan Najeriya ta gaza wajen sauke nauyin aiki da yiwa kasar nan hidima da ya rataya a wuyanta, ya sanya dakarun soji ke ci gaba da kai komo a tsakankanin al'umma.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasar ya bayar da shaidar hakan ne cikin wani faifan sautin murya yayin ganawa da manema labarai na kamfanin Arise TV a daren ranar Litinin din da ta gabata.

Shugaba Buhari tare da Sufeto Janar na 'yan sanda a fadar Villa

Shugaba Buhari tare da Sufeto Janar na 'yan sanda a fadar Villa
Source: Depositphotos

Jagoran na Najeriya ya yi furucin hakan ne yayin sake jaddada matsayar sa ta rashin goyon bayan samar da 'yan sandan jiha da wasu gwamnoni da kuma majalisar dokoki ta tarayyar Najeriya suka bukata tun a bara.

Cikin dalilan da shugaban kasa ya zayyana, ya ce akwai babbar barazana ta samar da 'yan sandan tare da mallaka ma su makamai karkashin kulawar gwamnoni a yayin da sai an kai ruwa rana wasun su ke iya biyan albashin ma'aikatan jihar su.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya ba na goyon bayan samar da 'yan sandan jiha - Buhari

Sakamakon yalwar arziki gami da dogaro da kai ta jihar Legas, shugaba Buhari ya yabawa gwamnan jihar, Akinwunmi Ambode, da kwazo bisa aiki ya sanya ya samar da wata hukumar tsaro mai lakabin Lagos State Neighborhood Corps.

Duk da kasancewar samar da 'yan sandan jiha muhimmin lamari ne mai tasiri gaske wajen habaka da ci gaban kasa, shugaba Buhari ya ce hakan ba zai sanya ya sauya ra'ayin sa kan barazanar da ka iya aukuwa yayin tabbatuwar hakan a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel