Lauyoyi sun fafata a kotu kan takaddamar sanya hijabi a makarantun jihar Ogun

Lauyoyi sun fafata a kotu kan takaddamar sanya hijabi a makarantun jihar Ogun

- A ranar Talata, lauyoyi biyu suka kusan baiwa hammata iska, inda suka fafata tare da musayar kalamai a babbar kotun jihar Ogun da ke Isabo, Abeokuta

- Lauyoyin sun fafata ne a yayin muhawarar shari'ar da ake yi kan sanya hijabi a makarantun gwanati na jihar

- A watan Disambar shekarar data gabata, wata yarinyar mai shekaru 19, Aisha AbdulAleem, ta shigar da gwamnati kara kan tauye mata hakki da aka yi na sanya hijabi

A ranar Talata, lauyoyi biyu suka kusan baiwa hammata iska, inda suka fafata tare da musayar kalamai a babbar kotun jihar Ogun da ke Isabo, Abeokuta, a yayin muhawarar shari'ar da ake yi kan sanya hijabi a makarantun gwanati na jihar.

A watan Disambar shekarar data gabata, wata yarinyar mai shekaru 9, da ke karatu a wata karamar makarantar sakandire ta jeka-ka-dawo, Aisha AbdulAleem, ta shigar da gwamnati kara kan tauye mata hakki da aka yi na sanya hijabi, inda ta bukaci a biyata fansar N1m.

Da ake sauraron shari'ar karo na biyu a ranar Talata, lauyoyin mai kara da wanda ake karar, Israel Awofeso da Sulaiman Akinbami, sun yi musayar yawu kan bukatar dage sauraron karar. Shari'ar dai ta samu halartar bangararorin addinai biyu, Musulmai da Kirista.

KARANTA WANNAN: Zargin sukar Buhari: Faifan sautin muryar Amaechi ba zai kawo baraka a APC ba - Minista

Lauyoyi sun yi musayar yawu a kotu kan takaddamar sanya hijabi a makarantun jihar Ogun

Lauyoyi sun yi musayar yawu a kotu kan takaddamar sanya hijabi a makarantun jihar Ogun
Source: Depositphotos

Lauyan wacce ta shigar da karar,Akinbami, ya roki kotu data saurari karar da idon basira tare da yanke hukunci cikin gaggawa, kasancewar dalibai wacce ya ce ba ta iya zuwa makaranta a yanzu sakamakon tauye mata 'yanci da akayi, tana da bukatar a kwatar mata 'yancinta.

Akinbami ya ce shari'ar ta shafi kusan daukacin al'ummar jihar ne musamman ma dalibai.

Sai dai lauyan wanda ke kare wanda ake karar, Awofeso, cikin fushi yace sam bai kamata a ci gaba da sauraron karar, kasancewar akwai rashin ladabi ga yarinyar da ta shigar da karar, kasancewar dokace ta gwamnati da aka sanyawa kowa.

Sai dai, mai sharia a kotun, Bamgbose Alabi, ya dai-daita hayaniyar inda ya sha alwashin yanke hukuncin shari'ar ba tare da bata lokaci ba. Ya dage sauraron karar har sai 16 ga watan Janairu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel