Ekweremadu da gwamnonin PDP na kudu maso gabas na yiwa Buhari aiki – BMO

Ekweremadu da gwamnonin PDP na kudu maso gabas na yiwa Buhari aiki – BMO

- Kungiyar labaran shugaba Buhari ta yaba da mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Ta bayyana cewa hatta ga yan takarar PDP a arewacin Najeriya na kokarin ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya zarce.

- Kungiyar tayi zargin cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da gwamnonin PDP a kudu maso gabas na yiwa shugaban kasar aiki

Kungiyar labaran shugaba Buhari wato Buhari Media Organisation (BMO) ta yaba ma abunda ta bayyana a matsayin mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta bayyana cewa hatta ga yan takarar Peoples Democratic Party (PDP) a arewacin Najeriya na kokarin ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress APC ya zarce.

Hakan na zuwa ne a lokacin da kungiyar tayi zargin cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da gwamnonin PDP a kudu maso gabas na yiwa shugaban kasar aiki.

Ekweremadu da gwamnonin PDP na kudu maso gabas na yiwa Buhari aiki – BMO

Ekweremadu da gwamnonin PDP na kudu maso gabas na yiwa Buhari aiki – BMO
Source: Facebook

Kungiyar masoyan Buharin ta yi al’ajabin dalilin da yasa yan takarar PDP ba sa yin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyarsu, Atiku Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Osun, Ondo, Ekiti da sauran Jihohin da babu zaben Gwamna a bana

A wani jawabu daga shugaban kungiyar, Niyi Akinsiju da sakataren kungiyar, Cassidy Madueke sun bayyana cewa alamun karbuwan da shugaban kasar ya samu tabbaci ne ga cewar gwamnonin PDP da yan takarar majalisar dokokin kasar a yankunan kasar na gudanar da kamfen da fasta mai dauke da hoton shi.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Ministan watsa labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce faifan muryar ministan zirga zirga, Rotimi Amechi da aka saki yana kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba zai ruguza mukaman APC ba.

Ministan wanda ya bayyana hakan a wata zantawarsa da manema labarai a ranar Talata a Abuja, ya ce faifan muryar da ake saki na daga cikin wani yunkurin na abokan hamayya da nufin kawo rudani a jam'iyyar APC da gwamnatin shugaban kasa Buhari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel