Zargin sukar Buhari: Faifan sautin muryar Amaechi ba zai kawo baraka a APC ba - Minista

Zargin sukar Buhari: Faifan sautin muryar Amaechi ba zai kawo baraka a APC ba - Minista

- Alhaji Lai Mohammed ya ce faifan muryar Rotimi Amechi da aka saki yana kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba zai ruguza mukaman APC ba

- Ministan ya ce faifan muryar da ake saki na daga cikin wani yunkurin na abokan hamayya da nufin kawo rudani a jam'iyyar APC da gwamnatin Buhari

- Lai Mohammed ya ce duk wanda yake son ya yada wani faifan murya ko bidiyo, to ya bayyanawa mutane makusudin yin hakan

Ministan watsa labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce faifan muryar ministan zirga zirga, Rotimi Amechi da aka saki yana kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba zai ruguza mukaman APC ba.

Ministan wanda ya bayyana hakan a wata zantawarsa da manema labarai a ranar Talata a Abuja, ya ce faifan muryar da ake saki na daga cikin wani yunkurin na abokan hamayya da nufin kawo rudani a jam'iyyar APC da gwamnatin shugaban kasa Buhari.

"Meye amfanin lalubo faifan murya tare da yadawa a kafafen sadarwa, sunyi hakan ne don kawo rudani a APC da gwamnatin Buhari? Me ya sa suke tunanin yin hakan zai ruguza mukamin jam'iyya mai mulki? Me zasu amfana da wannan abu da suka yi?"

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Tsohon shugaban PDP a Arewa ya koma APC, ya gana da Buhari

Zargin sukar Buhari: Faifan sautin muryar Amaechi ba zai kawo baraka a APC ba - Minista

Zargin sukar Buhari: Faifan sautin muryar Amaechi ba zai kawo baraka a APC ba - Minista
Source: UGC

Lai Mohammed ya ce duk wanda yake son ya yada wani faifan murya ko bidiyo, to ya bayyanawa mutane makusudin yin hakan, "idan ba haka bam, to su ci gaba da bata lokacinsu wajen yada faifan muryar wanda ba zai karesu da komai ba, munsan cewa wannan salon damfara ne."

Ministan ya kuma ce ci gaba da daukaka zargin da ake yiwa iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewar sun mallaki wani kaso mai tsoka a kamfanin sadarwa na 9Mobile da bankin Keystone, na daga cikin yunkurin da PDP ta shirya a Dubai, na yin batanci ga Buhari da iyalansa da nufin bakantasu a idanun 'yan Nigeria.

Ya ce dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya rasa samun kungiyar yakin zabe mai katabus, kuma duk wani yunkuri da suke yi na samun nasara kan jam'iyya mai mulki yaci tura, kuma ba zai tabbata ba.

Ministan ya kuma ce ya zama wajibi a jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan matakin da ya dauka na mayar da hankali kan aikinsa, mai makon mayar da hankali wajen yakin zaben tazarcensa a zaben watan Fabreru mai zuwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel