Buhari ya karbi wasika daga shugabannin kasashen Kenya da Guinea

Buhari ya karbi wasika daga shugabannin kasashen Kenya da Guinea

Mun ji cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi kira ga shugabannin da ke kasasshen Afrika da su dage wajen kokarin gina kasa. A cewar sa wannan ne kurum zai kawo cigaba a Nahiyar.

Buhari ya karbi wasika daga shugabannin kasashen Kenya da Guinea

Shugaban kasa Buhari yayi kira ga shuganannin Afrika
Source: Depositphotos

A jiya ne Buhari ya karbi wasiku daga Jakadan kasar Guinea da ke Najeriya watau Siaka Cissoko. Jakadan ya ziyarci shugaban Najeriyar ne a ofishin sa da ke fadar Aso Villa. Shugaban ya nemi hadin kan takwaran na sa na kasar Guinea.

Buhari ta bakin mai magana da yawun sa watau Garba Shehu, ya taya shugaban kasa Kasar Guinea murnar irin nasarar da yake samu tare da kuma yin alkawarin ba kasar duk wata gudumuwar da ta ke bukata a zaben da za tayi kwanan nan.

KU KARANTA: 2019: Wani Masoyin Buhari ya bar APC ya shiga jirgin Atiku

A jawabin da Malam Garba Shehu ya fitar jiya a Abuja, shugaban ya kuma yi kira ga Alpha Conde cewa duk wani gyara da zai yi wa tsarin siyasar kasar Guinea, dole ya zama an ingantar rayuwar jama’a tare da ganin ra’ayin su yana tasiri a zabe.

Buhari ya bayyana cewa dole sai shugabannin kasashen Afrika sun gina kasar su idan har ana so a ga cigaba da fuskar tattalin arziki da tsaro da zaman lafiya. A karshe ya kuma nemi kasashen su hada kai musamman a harkar albarkatun kasa.

Har wa yau, shugaba Muhammadu Buhari ya karbi wasika ta musamman daga jakadan kasar Kenya, Dr Wilfred Gisuka Machage. Buhari ya nuna jin dadin sa game da irin cigaban da aka samu a Kenya ta fuskar siyasa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel