Buhari ya bayyana abinda yasa bai tsige Buratai, Saddique da sufetan Yansanda ba

Buhari ya bayyana abinda yasa bai tsige Buratai, Saddique da sufetan Yansanda ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa har yanzu bai cire manyan hafsoshin hukumomin tsaron Najeriya ba, inda ya danganta dalilin hakan da yaki da ta’addanci da suke yi, idan ya ciresu a yanzu zai lalata duk wani shiri da suke yi.

Buhari ya bayyana haka ne cikin wata ganawa da yayi da gidan talabijin na Arise TV, inda yace nan bada jimawa ba zai yanke hukunci game da wa’adin mulkin babban sufetan Yansandan Najeriya Ibrahim Idris da lokacin saukarsa yayi, walau ya kara masa ko kuma ya saukeshi.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya sanya labule da El-Rufai a fadar Villa

Buhari ya bayyana abinda yasa bai tsige Buratai, Saddique da sufetan Yansanda ba

Buhari da hafsoshin tsaro
Source: UGC

Legit.com ta ruwaito Buhari yace a matsayinsa na tsohon shugaban kasa a mulkin Soja, tsohon minista kuma tsohon gwamna, bai kamata yana yanke hukunci cikin hanzari ko gaggawa ba, kamata yayi sai ya fahimci matsala kafin ya yanke hukunci akai.

“Idan ka cire hafsoshin rundunonin Soji da babban sufetan Yansanda a yanzu da ake tsaka da yaki da ta’addanci ba tare da jiran lokacin daya kamata ba, zaka kirkiri matsala a aikin tsaro gaba daya, saboda akwai masu son darewa mukaman nan dayawa.

“Mutanen nan da na zaba a matsayin shuwagabannin tsaro Najeriya, ban sansu ba, na duba tarihinsu aikinsu ne kawai, kuma ina tunanin sune mafi nagarta a cikin sauran, za’a iya cewa aikinsu bai kai ga yadda nake so ba, amma na dauki nauyin duk abinda suka yi ko suka gaza.” Inji shi.

Da yake tsokaci kan zargin da ake yi na cewa yan Arewa ne suke shugabantar dayawa daga cikin hukumomin tsaron Najeriya, suke shugabancin hukumomi 14 cikin 17 na Najeriya, sai Buhari yace ana lura da biyayya da kuma aminci ne kafin a nada irin wannan mukami.

Game da batun ya ware al’ummar kabilan Ibo kuwa, Buhari yace kuri’u dubu dari da casa’in da takwas (198,000) kacal ya samu daga yankin Inyamurai gaba daya, amma duk da haka ya basu ministocin kasashen waje, masana’antu, kimiyya da fasaha, da kwadago ba tare da saninsu ba ko kadan.

“Baya ga haka na nada ma ma’aikatun nan kananan ministoci daga yankin Arewa, yankin da nafi samun kuri’u, wani irin adalci kuma ake so na yi musu banda wanda nayi a yanzu?” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel