Hukumar INEC ta bullo da wani muhimmin sauyin ga yadda za’a gudanar da zaben 2019

Hukumar INEC ta bullo da wani muhimmin sauyin ga yadda za’a gudanar da zaben 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta sanar da soke maganan kara yawan rumfunan zaben da jama’a zasu kada kuri’a, inda tace koda za’a samu wannan cigaba, ba dai a yayin zaben 2019 ba, kila sai dai a gaba, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.com ta ruwaito guda cikin kwamishinonin hukumar, Farfesa Okechukuw Ibeanu ne ya bayyana haka a ranar Talata 8 ga watan Janairu a babban birnin tarayya Abuja yayin ganawa da yan jaridu da hukumar ta saba a duk bayan watanni hurhudu.

KU KARANTA: Yan dagajin Malamai ne ke janyo mana rikici a Najeriya – Sultan

Hukumar INEC ta bullo da wani muhimmin sauyin ga yadda za’a gudanar da zaben 2019

Zabe a Najeriya
Source: Depositphotos

A jawabin nasa, Farfesa Ibeanu yace za’a cigaba da tattara sakamakon zabe da hannu ne ba da na’urar kwamfuta ba, ba kamar yadda gyare gayren da majalisa tayi ma dokokin zabe ba, saboda har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari bai rattafa hannu akan dokar ba.

Bugu da kari kwamishinan yace a wannan karon za’a gudanar da tantancewa tare da jada kuri’a ne a tare, ma’ana da an tantance mutum zai kada kuri’arsa, ba kamar yadda aka yi a zaben 2019 ba, inda sai an yi dogon jira bayan tantancewa kafin a kada kuri’a.

Wani sassauci da hukumar zaben ta kara yi ma yan Najeriya shine, mutum zai iya yin zabe koda ba shi da katin zabe idan har sunansa ya bayyana a cikin jerin sunayen dake cikin rajistan hukumar na wannan akwatin zabe.

Amma fa har sai ire iren mutanen nan sun ajiye lambar wayarsu, tare da kuma shaidar yatsunsu, ta yadda za’a iya ganesu a gaba idan sun sake dawowa kada kuri’a, kamar yadda Farfesan ya tabbatar.

Idan za’a tuna, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattafa hannunsa akan kwaskwararren kundin dokar zabe da yan majalisu suka kammala aiki akansa, inda yace yayi hakan ne saboda zabe bai wuce sauran watanni uku ba a lokacin da aka kawo masa kundin, don haka idan ya sanya hannu zai lalata ma INEC shirinta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel