Uwargidan gwamna Bagudu ta fara yiwa Buhari kamfen din gida-gida a Kebbi

Uwargidan gwamna Bagudu ta fara yiwa Buhari kamfen din gida-gida a Kebbi

- Uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Dr. Zainab Bagudu ta fara bin gida-gida domin yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen don ganin ya zarce a zaben 2019

- Ta ce za ta tara mata da matasa a yankin arewa maso yamma don ganin sun zabi shugaba Buhari a 2019.

- Zainab ta kara da cewa APC za ta yi dogaro da karfin mata da matasa a yakin don ganin ta samu kuri’u mafi yawa

Uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Dr. Zainab Bagudu ta fara bin gida-gida domin yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen don ganin ya zarce a zaben 2019.

Misis Bagudu, wacce kwanan nan aka nada ta a matsayi jagorar kamfen din shugaban kasa na mata da matasa a yankin arewa maso yamma ta bayyana a lokacin hira da yan jarida a gida gwamnatin jihar Kebbi cewa za ta tara mata da matasa a yankin arewa maso yamma don ganin sun zabi shugaba Buhari a 2019.

Uwargidan gwamna Bagudu ta fara yiwa Buhari kamfen din gida-gida a Kebbi

Uwargidan gwamna Bagudu ta fara yiwa Buhari kamfen din gida-gida a Kebbi
Source: Twitter

Tace APC za ta yi dogaro da karfin mata da matasa a yakin don ganin ta samu kuri’u mafi yawa.

KU KARANTA KUMA: Rabiu Biyora ya watsar da tafiyar Buhari bayan ya gana da Atiku

Tace nasarorin da shugaba Buhari ya samu a wajen yin ayyukan ci gaba, bayar da talafi da kuma kokarin uwargidansa, Dr. Aisha Buhari wajen inganta rayuwar mata da yara a fadin kasar zai taimaka masa wajen yin nasara a zaben.

Dr Zainab tace: “ Za mu hadu da mutane a gida-gida domin wayar masu da kai, don nuna masu nasarorinmu. Mun rigada mun fara kamfen dinmu domin tara mata da matasa a yankin don su zabi Buhari da APC, wasu daga cikin shirye-shiryenmu a bayyane sune sannan wasu a boye suke don muyi nasara a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel