Da duminsa: Tsohon shugaban PDP a Arewa ya koma APC, ya gana da Buhari

Da duminsa: Tsohon shugaban PDP a Arewa ya koma APC, ya gana da Buhari

- Sanata Babayo Gamawa, ya sauya sheka, inda ya koma jam'iyya mai mulki ta APC tare da ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Kafin komawarsa APC, Sanata Gamawa, shine mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa reshen Arewa

- Jam'iyyar PDP ta koriMr Gamawa, sakamakon zarginsa da gaza aiwatar da aikin ofishinsa da kuma cin amanar jam'iyyar

Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa reshen shiyyar Arewa, Babayo Gamawa, wanda jam'iyyar ta kora sakamakon zargin cin amana, ya sauya sheka, inda ya koma jam'iyya mai mulki ta APC.

A ranar Litinin ne jam'iyyar PDP ta kori Mr. Gamawa, bisa babban zargin da take masa na gaza aiwatar da ayyukan ofishinsa, da kuma yiwa jam'iyyar APC aiki ta karkashin kasa.

Sakataren watsa labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan wanda ya sanar da matakin korar, ya ce Mr Babayo ya fuskanci hukuncin ne bayan wani taro da kwamitin zartaswa na jam'iyyar ya gudanar kan makomarsa.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Buhari zai gabatar da kudurin dokar sabunta albashi ga majalisar tarayya

Da duminsa: Tsohon shugaban PDP a Arewa ya koma APC, ya gana da Buhari

Da duminsa: Tsohon shugaban PDP a Arewa ya koma APC, ya gana da Buhari
Source: Twitter

A ranar Talata ne aka sanar da komawar Mr Babayo jam'iyyar APC, ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mr Femi Adesina.

Mr Adesina ya wallafa hotunan Mr Gamawa da Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, a lokacin da suka ziyarci shugaban kasar a gidansa da ke cikin fadar shugaban kasa.

"Shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin sabon shiga jam'iyyar APC, wanda kuma shine tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa reshen jihar Arewa Sanata Babayo Garba Gamawa tare da Hon. Kaulaha Aliyu da kuma gwamnan jihar Bauchi, a fadar shugaban kasa," a cewar Adesina.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel