A karo na 2: Mohammed Salah ya lashe kambun gwarzon dan wasan Afrika

A karo na 2: Mohammed Salah ya lashe kambun gwarzon dan wasan Afrika

- Mohammed Salah, ya sake lashe kambun gwarzon dan kwallon nahiyar Afrika na shekarar 2018 a karo na biyu, bayan lashe kambun a 2017

- Salah ya samu nasarar doke abokin taka ledarsa na Liverpoo, Sadio Mane da kuma dan wasan gaba na kungiyar Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang

- Wannan nasarar ta Salah, ta biyo bayan amincewa kasar Masar marabtar wasan cin kofin kasashen Afrika na shekarar 2019

Daya daga cikin manyan 'yan wasan taka leda na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohammed Salah, ya sake lashe kambun gwarzon dan kwallon nahiyar Afrika na shekarar 2018 a karo na biyu, bayan lashe kambun a 2017.

Dan wasan gaban na kasar Masar, ya samu nasara ne bayan da aka zabe shi a matsayin wanda ya lashe kambun karramawar a bukin karrama 'yan wasa na shekarar 2018, da hukumar kwallonnkafa ta Afrika (CAF) ta shirya a Dakar, a ranar Talata.

Salah ya samu nasarar doke abokin taka ledarsa na Liverpoo, Sadio Mane da kuma dan wasan gaba na kungiyar Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, wadanda suka bugawa Senegal da Gabon a bangaren kasashe.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Buhari zai gabatar da kudurin dokar sabunta albashi ga majalisar tarayya

A karo na 2: Mohammed Salah ya lashe kambun gwarzon dan wasan Afrika

A karo na 2: Mohammed Salah ya lashe kambun gwarzon dan wasan Afrika
Source: Twitter

Ko a shekarar 2017 data gabata, Salah ya samu nasara akan yan wasan biyu a kuri'un da aka kada, inda masunhoras da yan wasa 56 daga cikin mambobin hukumar CAF suka zabe shi.

Sai dai, Aubameyang ya kasance a cikin jerin masu nasara guda uku na farko har sau 5, inda ya taba lashe kambun sai daya a shekarar 2015.

Hakika wannan nasara da Salah ya samu, ba karamar nasara bace ga wasan taka leda a kasar Masar, musamman yadda aka amincewa kasar Masar din marabtar wasan cin kofin kasashen Afrika na shekarar 2019.

Da farko kasar Kamaru ce aka amince mawa ta marabci gasar, amma aka kwace damar daga hannunta, sakamakon tafiyar hawainiya da shirye shiryenta yake yi.

Masar ta samu damar ne bayan da ta doke kasar Afrika ta Kudu a wajen zabe, kasar da ta bukaci a bata damar marabtar gasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel