Tawagar PDP ta shilla Amurka, sai dai babu Atiku cikinsu, ko me ya hanashi oho

Tawagar PDP ta shilla Amurka, sai dai babu Atiku cikinsu, ko me ya hanashi oho

- Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyar PDP baiji dadin tafiyar da jam'iyar sa zatayi batare dashi ba

- Jam'iyar ta PDP zatayi tafiya zuwa Washington DC dan gudanar da wani taro

- Maimakon jam'iyar ta dauki Atiku Abubakar saita dauki Peter Gregory Obi

Tawagar PDP ta shilla Amurka, sai dai babu Atiku cikinsu, ko me ya hanashi oho

Tawagar PDP ta shilla Amurka, sai dai babu Atiku cikinsu, ko me ya hanashi oho
Source: Facebook

Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyar PDP Atiku Abubakar baiji dadin tafiyar da jam'iyar sa zatayi batare dashi ba.

PDP zata gudanar da taron nata a sati mai zuwa a kasar Washington DC akan makomar alakar US da Najeriya anan gaba.

A maimakon jam'iyar ta dauki Atiku Abubakar a wannan tafiya sai ta dauki Peter Gregory Obi.

Mr Obi zai zamo bako a Center for Strategic & international studies (CSIS) inda zasu tattauna akan sha'anin tattalin arziki da kuma tsaro da kuma abinda yake gani dangane da alakar US da Najeriya anan gaba.

DUBA WANNAN: Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

Za'a gudanar da taron a ranar Talata 15 ga watan Junairu shekara ta 2019.

Rashin halartar wannan taro da Atiku zaiyi ya tabbatar da hasashen da akeyi na cewar yana da case da US.

Bada dadewa ba mai magana da yawun masu yiwa Buhari kamfe babban lauya Festus Keyamo yace Alhaji Atiku Abubakar yana da yar tsama tsakanin sa da US duk ranar daya shiga kasar ba'a matsayin dan takara ba zai gamu da hukunci.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel