Albashin N30,000: Shugaba Buhari ya nada Alfred Rewane ya duba yadda za'a fara biya

Albashin N30,000: Shugaba Buhari ya nada Alfred Rewane ya duba yadda za'a fara biya

-

-

-

Albashin N30,000: Shugaba Buhari ya nada Alfred Rewane ya duba yadda za'a fara biya

Albashin N30,000: Shugaba Buhari ya nada Alfred Rewane ya duba yadda za'a fara biya
Source: UGC

- Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kafa sabon kwamiti akan karin albashi

- Bayan kaddamar da sabon albashi gwamnati zata kulla wata yarjejeniyar sulhu tsakanin ta da ma'aikata

- An bawa wannan kwamiti wata 1 ya tattara duk wasu bayanai daya kamata ya mika

A ranar Laraba shugaban kasa Muhammad Buhari ya kafa wani kwamiti akan karin albashi.

Da yake ganawa da yan kwamitin a Villa dake Abuja Buhari yace bayan an kaddamar da batun karin albashin gwamnati zatayi wata yarjejeniyar sulhu tsakanin ta da ma'aikatan da suka riga suka fara karbar sabon tsarin albashin.

A bangaren sa yace yanada muhimmanci wadanda abin ya shafa susan abinda ake ciki kar lokaci yazo suce basusan komai akai ba.

Duba da cewa karin albashi na karshe da Najeriya tayi anyi shine tun a shekara ta 2011 saboda haka ya zama dole a dunga tunasarwa don gujewa inkari a bangare gwamnatin.

Yace "Wannan dalilin ne ya sanya gwamnati ta kafa wannan kwamiti akan karin albashi da kuma wasu shawarwari daya kamata ayi duba akansu.

DUBA WANNAN: Matsalar shaye-shayen mata ta fara sauki a Kano, sai dai, Katsina ta dauka

"Wannan kwamiti ya miko wasu shawarwarin wanda a yanzu haka muna dubawa muna mataki na karshe da zarar mun kammala zamu mikiwa majalisa wannan bukata.

"Yanada muhimmanci mu sanar da cewa duk da cewa maganar karin albashi da shiga cikin jerin abubuwan da za'a kaddamar,muna ganawa da gwamnonin jihohi akan hakan.

Ana bukatar wannan kwamiti ya tattara duk wasu bayanai daya kamata ya mika a cikin wata Daya.

A cikin awanni 24 da suka gabata ne kwamitin da kuma gwamnati suka amince a mikawa majalisa wannan batu daga yanzu zuwa 23 ga watan Junairu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel