An kammala wasu sabbin tashoshin lantarki 8 da biliyoyin kudi ana dab da zabe

An kammala wasu sabbin tashoshin lantarki 8 da biliyoyin kudi ana dab da zabe

- Ana bukatar lantarki Megawatt 50,000 a Najeriya

- Har yanzu 4,000 kadai muke iya saarwa

- An kammala wasu manyan tashohin a Neja Delta

An kammala wasu sabbin tashoshin lantarki 8 da biliyoyin kudi ana dab da zabe

An kammala wasu sabbin tashoshin lantarki 8 da biliyoyin kudi ana dab da zabe
Source: Facebook

Bayan shafe shekaru hudu ana aiki, da ma kashe biliyoyin Nairori, shirin gwamnatin Tarayya na NIPP ya samar da karin Megawatt daruruwa wanda ya hada da 750MW a Olorunsogo 11, sai 450MW Sapele, 434MW Geregu 11, 450MW Omotosho 11, 450MW Ihovbor, 450MW Alaoji, 563MW Calabar da ma 225MW Gbarain.

Kamfanin Lantarki na NDPHC kuma, ya kara wayoyin har tsawon 2,194km wadanda zasu dauki 330KV transmission da ma kuma 809km, masu daukar wutar 132KV.

Sai kuma 2,600km of 11kv na 1,700km, 33kv shima wanda zai taso ya kawo wutar birane. Wannan na nuin kasar nan zata sake samun karin wutar lantarki nan ba da dadewa ba. Duka-duka dai shirin, zai samar da karin 265MW kan wanda ake dasu a halin yanzu.

DUBA WANNAN: Hukuma tayi holin 'yan ta'adda bakwai a jihar tsakiyar Najeriya

Dama dai kasar nan na kan ganiyar farfadowa daga shekaru kusan 40 na mulkin soji, inda komai ya tsaya cak, aka daina zuba jari da manyan ayyukan ci gaban kasa.

Tun hambaras da mulkin faras hula na Shagari dai, babu wani muhimmin aiki da kasar nan ta iya cimma da sunan wadanda manyan iyaye irinsu Awwalawo da Azzikiwe da Sardauna suka dauko, wasoso kawai aka yi tayi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel