Yadda aka yi rajistar zabe jiha bayan jiha a fadin kasar nan

Yadda aka yi rajistar zabe jiha bayan jiha a fadin kasar nan

- Hukumar zabe ta fitar da yawan mutanen da sukayi rajistar zabe

- Jihar Legas ce da mutane mafi yawa da zasu kada kuri'u a zaben mai zuwa

- Jimillar mutanen da zasu yi zaben a jihohi 36 da birnin tarayya ya kama 84,004,084

Yadda aka yi rajistar zabe jiha bayan jiha a fadin kasar nan

Yadda aka yi rajistar zabe jiha bayan jiha a fadin kasar nan
Source: Depositphotos

Hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar da yawan mutanen da sukayi rajistar zabe a jihohi 36 na kasar nan tare da birnin tarayya.

Jihar Abia na da 1,932,892, jihar Adamawa na da 1,973,083, jihar Akwa Ibom na da 2,119,727 sai jihar Anambra mai 2,447,994.

Jihar Bauchi na da mutane 2,462,843 wadanda sukayi rajistar, jihar Bayelsa na da 923,182 inda jihar Benue ke da 2,480,131.

Jihar Borno na da mutane 2,315,956 ,sai jihar Cross River da ke da 1,527,289. Jihar Delta na da mutane 2,845,274 ,jihar Ebonyi na da 1,459,933, jihar Edo kuma na da 2,210,534.

Jihar Ekiti na da mutane 909,967 da sukayi rajistar zabe, jihar Enugu ce take da 1,944,016 sai babban birnin tarayya Abuja da ke da mutane 1,344,856.

Jihar Gombe na da mutane 1,394,393 da sukayi rajistar zabe, jihar Imo na da 2,272,293, jihar jigawa na da 2,111,106 sai jihar Kaduna da ta tashi da 3,932,492.

DUBA WANNAN: Hukumci: An kulle matsashin da ya tsiyayar wa da makwabcinsa ido

Jihar Kano na da mutane 5,457,747 da sukayi rajistar zabe, jihar Katsina na da 3,230,230, jihar Kebbi na da 1,806,231, jihar Kogi na da 1,646,350 sai jihar Kwara da take da 1,406,457.

Jihar Legas na da mutane 6,570,291 wadanda sukayi rajistar zabe, jihar Nasarawa na da 1,617,786, jihar Niger na da 2,390,035 sai jihar Ogun da ke da 2,375,003.

Jihar Ondo na da mutane 1,822,346 da sukayi rajistar zabe, jihar Osun na da 1,680,498, jihar Oyo na da 2,934,107 sai jihar Plateau da ke da 2,480,455.

Jihar Rivers na da mutane 3,215,273 da sukayi rajistar zabe, jihar Sokoto na da mutane 1,903,166, jihar Taraba na da 1,777,105, jihar Yobe na da 1,365,913 sai jihar Zamfara da ke da mutane 1,717,128 da suka yi rajistar zabe.

Jimillar mutanen da sukayi rajistar zabe a fadin kasar nan sune 84,004,084.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel