Aikin assha: Dan sanda ya harbe direbobi 2 saboda sun ki ba shi rashawa

Aikin assha: Dan sanda ya harbe direbobi 2 saboda sun ki ba shi rashawa

Mun samu labarin cewa wani dan sandan Najeriya da ke da matsayi na Isifecta ya harbi wasu direbobin motocin haya su biyu saboda sun hana shi kudin cin hanci da rashawa da ya bukata daga wurin su a garin Lokoja, jihar Kogi.

Majiyar mu ta Daily Trust ta ruwaito mana cewatun farko dai dan sandan ya tsaida direbobin ne akan hanya inda ya bukaci su bashi cin hanci amma su kuma suka ki wanda hakan ya jaza masu hatsaniya a tsakanin su.

Aikin assha: Dan sanda ya harbe direbobi 2 saboda sun ki ba shi rashawa

Aikin assha: Dan sanda ya harbe direbobi 2 saboda sun ki ba shi rashawa
Source: Twitter

Legit.ng Hausa ta samu cewa kamar yadda muka samu, rikicin tsakanin su ne yayi tsanani inda har direbobin suka tsere zuwa tashar motar su inda suke lodi amma 'yan sandan suka bi su kuma har ma suka harbe su.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ta Lokoja, Mista William Aya ya tabbatar da aukuwar lamarin inda kuma ya bayar da tabbacin yin adalci a rundunar ga wadanda wadanda lamarin ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel