Yanzu haka: Jiragen yakin sama 2 na barin wuta a dajin Sambisa

Yanzu haka: Jiragen yakin sama 2 na barin wuta a dajin Sambisa

Yanzu haka dai rundunar ta tabbatar da jiragen yakin su samfurin Mi35m, da Alpha Jets da ma sauran jiragen yakinsu yanzu haka suna can suna ta barin wuta a Arewa maso gabashin Najeriya.

Da yake jawabi ga mayakan a birnin Maiduguri, Babban Hafsan Hafsoshin rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar, yace ko kadan hadarin jirgin yakin su samfurin Mi35m da ya auku kwanan nan a Damasak ba zai sanyaya masu gwiwa ba.

Yanzu haka: Jiragen yakin sama 2 na barin wuta a dajin Sambisa

Yanzu haka: Jiragen yakin sama 2 na barin wuta a dajin Sambisa
Source: Twitter

KU KARANTA: Yadda 'yan kwadago suka shirya dagulawa Buhari lissafi

Yace yanzu suna cikin yaki ne kuma kamar sauran al'amuran rayuwa shima na da nasa hadurran, Amma wannan ba zai zama wani abun da ka iya kawo cikas a kokarin gamawa da burbushin mayakan.

Haka zalika a cewar sa, rundunar sojojin saman Najeriya tace zataci gaba da fatattakar mayakan Boko Haram har sai an kawo karshensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel