Wani gwamna a arewa yace ba zai iya biyan ma'aikata sabon tsarin albashi na N30,000

Wani gwamna a arewa yace ba zai iya biyan ma'aikata sabon tsarin albashi na N30,000

Gwamnan jihar Benue dake a arewa ta tsakiyar Najeriya, Samuel Ortom ya bayyana cewa shi fa ba zai iya biyan mafi karancin albashi na Naira dubu talatin ga ma'aikatan gwamnatin jihar kamar yadda shugaba Buhari ke shirin maidawa doka.

Mista Ortom dai ya bayyana hakan ne a ranar Talatar da ta gabata a garin Makurdi lokacin da yake jawabi ga shugabannin kungiyar kwadago watau Nigeria Labour Congress (NLC) a jihar.

Wani gwamna a arewa yace ba zai iya biyan ma'aikata sabon tsarin albashi na N30,000

Wani gwamna a arewa yace ba zai iya biyan ma'aikata sabon tsarin albashi na N30,000
Source: UGC

KU KARANTA: Kiristocin Kano sun bayyana wanda za su zaba a 2019

Legit.ng Hausa ta samu cewa Gwamnan ya bayyana cewa hakikanin gaskiya yana tausayawa ma'aikatan jihar game da jinkirin dabbaka karin albashin duk da dai cewa shi jihar sa bata iyawa saboda dalilai na rashin kudi.

Gwamna Ortom ya kara da cewa shi idan da so na zama samu to da mafi karancin albashin 'yan jihar ma sai ya wuce Naira dubu 30 din da ake magana to amma saboda rashin kudin da suke fama da shi, hakan ba zai yiwu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel