Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

- Raha-Alqunun ta tsere bayan tayi ridda daga Saudiyya

- Mahaifinta gwamna ne a kasar, kuma yace a kamo ta

- A Saudiuua ana yawan samun irin wannan, sai dai matan suna cikin hadari

Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa
Source: UGC

Wannan karon dai, kasar Saudiyya tayi tsit kan batun riddar wata budurwa, 'yar shekara 18 da haihuwa, wadda iyayenta ke nema ruwa a jallo, ita kuwa ta haye jirgi ta tsere Australia.

Mahukuntan Saudiyyar dai sun kwace Fasfonta da saukarsu kasar Thailand shan mai, suka ce kuma zasu maida ta gida ta kari, lamari da ya razana ta matuka har ta fito neman taimakon duniya.

Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa
Source: Twitter

A cewarta dai, muddin hukumomi suka kama ta suka mayar wa iyayenta, to kuwa kashinta ya bushe, domin kuwa kashe ta zasu yi, bayan da ta bayyana karara cewa bazata yi addinin Islaama ba.

A kasar Saudiyya dai, muddin mutum yayi ridda kashe shi ake yi ta hanyar fille kai, an kuwa kashe da dama ta wannan hanya, lamari da yasa mutane da yawa ke boye wannan ridda tasu koda kuwa sun tabbatar su ba musulmi bane.

Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa
Source: Twitter

Ilhadi dai, ya cika gidajen musulmi, sai dai da yawa na tsoron su fiddo kansu su bayyana, saboda tsoron kaifi, wanda hakan yasa ake samun munafukai da yawa tun zamanin annabi, cikin addinin, saboda shi dai addinin, shiga ce babu fita, mutu-ka-raba.

Bayan da duniya ta farga da batun Rahaf Muhammad Alqunun, sai aka yi caa kan majalisar dinkin duniya da ma sauran masu kare hakkin dan-Adam, kan lallai su bar yarinyar ta karasa kasar da za'a bata hakkokinta a matsayin dan-Adam, kar a maida ta gida su gille mata kai.

Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa
Source: Twitter

Daga karshe, hukumomin Thailand, sunsha alwashin bazasu taba bari a kama Rahaf ba, a maida ta Saudiyya, ganin yadda ake gunduwa-gunduwa da mutane a kasar, kamar yadda aka yi wa Jamal Khashoggi, bayan da ya bar kasar da zimmar tona Saudiyyar.

A kasashen Hausa ma, ana samun irin wadannan lamurra na masu barin addini, a jihohin da ake shari'ar Islama, lamari dake quntata wa masu son ayi shari'ar Islama, daga malamai da ma 'yan gari, ganin gwamnatin Tarayya ba ta Islama bace.

DUBA WANNAN: Siyasar Yanki: Hanyoyi 10 da Rabi'u Kwankwaso zai iya koyar siyasa daga Malaminta Jagaba Bola Tinubu

Koda yake Qur'ani ya baiwa kowa 'yancin yin addininsa, hadisi kuwa cewa yayi duk wanda ya bar addinin Islama a kashe shi, lamari da ya zama sharia a doka shekaru 1,400, kuma ake aiki dashi, don dai addinin ya maye yankunan duniya.

Matsalar itace, shi wanda aka haifa cikin addinin, yana da yancin ya farka yace baya yi, ko kuwa sai dai ya zauna ya mutu cikin addinin, koda kuwa bai yarda da dokoki ko labarukan tsoratarwar addinin ba?

Wannan shine kalubalen addinin Islama a wannan zamani.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel