Na yiwa yan Igbo adalci duk da karancin kuri’unsu gare ni – Buhari

Na yiwa yan Igbo adalci duk da karancin kuri’unsu gare ni – Buhari

- Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya yi raddi ga wadanda ke sukarsa akan zargin nunawa yan Igbo wariya

- Buhari yace duk da cewar ya samu kuri’u mafi karanci daga mutanen yankin a lokain zaben 2015, bai nuna son kai ba a wajen nade-naden mukamansa

- Dan takartar na APC yace idan har aka sake zabarsa, ba zai dauki dogon lokaci ba wajen kafa majalisarsa

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya yi raddi ga wadanda ke sukarsa akan zargin nunawa yan Igbo wariya.

Shugaban kasar yace duk da cewar ya samu kuri’u mafi karanci daga mutanen yankin a lokain zaben 2015, bai nuna son kai ba a wajen nade-naden mukamansa.

Na yiwa yan Igbo adalci duk da karancin kuri’unsu gare ni – Buhari

Na yiwa yan Igbo adalci duk da karancin kuri’unsu gare ni – Buhari
Source: Depositphotos

Yayi Magana nea wani hra da Arise TV a ranar Litinin, 7 ga watan Janairu.

Sugaban kasar yace idanhar aka sake zabarsa, ba zai dauki dogon lokaci ba wajen kafa majalisarsa.

A wani lamari na daban, mun ji cewa babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa aminci da gaskiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari shine abunda yasa ya zamo dan takarar da ba za a iya kayar da shi ba a zabe 2019.

KU KARANTA KUMA: Ka ajiye kudi akan tebur tare da Buhari a daki, za ka ga kudinka idan ka dawo - Tinubu

Tinubu ya yi jayayyar cewa halayyar manyan yan takarar da ke kan gaba a zabe mai zuwa wato Shugaba Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar basu yi kama ba ta ko ina.

Da yake jawabi a Lagas a ranar Talata, 8 ga watan Janairu ta jami’in labaransa, tsohon gwamnan ya ba shugaba Buhari tabbacin cewa ya amshi aikin da ya bashi na kamfen dins da hannu bibbiyu kuma zai yi aiki don kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel