Dalilin da ya sanya ba na goyon bayan samar da 'yan sandan jiha - Buhari

Dalilin da ya sanya ba na goyon bayan samar da 'yan sandan jiha - Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce duk da kasancewar samar da 'yan sandan jiha muhimmin lamari ne mai tasiri gaske wajen habaka da ci gaban kasa, hakan ba zai sanya ya sauya ra'ayin sa na nuna rashin goyon baya.

Cikin kalaman sa shugaba Buhari ya bayyana cewa, samar da 'yan sandan jiha zai matukar kara inganci da habakar nagarta ta tsaro a kasar nan, sai dai hakan ba zai yiwu ba sakamakon wasu dalilai da ka iya janyo kwan-gaba-kwan baya na ci gaban kasa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya yi wannan furuci ne cikin wani faifan sautin murya yayin ganawa da manema labarai na kamfanin Arise TV a daren jiya na Litinin.

Dalilin da ya sanya ba na goyon bayan samar da 'yan sandan jiha - Buhari

Dalilin da ya sanya ba na goyon bayan samar da 'yan sandan jiha - Buhari
Source: UGC

Ya ce babban kalubalen da wannan lamari zai fuskanta bai wuci gazawar mafi akasarin gwamnonin kasar nan ba wajen sauke nauyin albashin ma'aikata da ya rataya a wuyan su.

Sai dai ya yabawa kwazon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, da yalwar arzikin jiharsa ta yi tasiri wajen samar da wata hukumar tsaro ta jiha mai lakabin Lagos State Neighborhood Corps.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ba za ta haramtawa manema labarai damar gudanar da aikin su ba - Ministan Al'adu

"A yayin da wasu daga cikin gwamnonin jihohin kasar nan ke fama wajen sauke nauyin albashin ma'aikata, ba zai yiwu a sake jibga ma su nauyin jami'an tsaro ma su rike da makamai ba tare da biyan su albashi ba."

Shugaban kasar ya kuma bayyana takaicin sa dangane da yadda jami'an tsaro na 'yan sanda suka gaza sauke nauyin da rataya a wuyan su, da a halin yanzu dakarun ke kawo ma su dauki wajen tabbatar da tsaro a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel