Ganduje zai biya N30,600 a matsayin karancin albashin ma'aikata

Ganduje zai biya N30,600 a matsayin karancin albashin ma'aikata

A yayin da hadaddiyar kungiyar kwadago ke fama da wasu gwamnonin jihohin Najeriya kan batun biyan karancin albashin da aka amince na naira dubu talatin da(N30,000), wasu gwamnonin kuwa maraba suka yi da wannan sabon tsari.

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa idan dokar sabon karancin albashi a Najeriya ta fara aiki, zai biya abinda ya haura adadin da dokar ta tanada a biya kowanne ma’aikacin gwamnati a kowanne wata.

KU KARANTA: Karancin albashi: Shehu Sani ya taya yan kwadago zanga zanga

Ita dai wannan dokar sabon tsarin karancin albashi da ake ta takaddama akanta ta tanadi kudi naira dubu talatin a matsayin adadin kudin da za’a fara biyan karamin ma’aikaci sabon dauka aiki a kowacce ma’aiakata a Najeriya, ta gwamnati ko ta yan kasuwa.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne ta bakin mataimakinsa, Alhaji Nasiru Gawuna, wanda ya bayyana cewa gwamnatin jahar Kano za ta kara naira dari shida (N600) akan kudin da aka yanke, watau karancin albashin ma’aikaci a jahar Kano zai kai naira dubu talarin da dari shida kenan (N30,600).

Jawabin haka ya fito ne daga bakin Gawuna a lokacin da yake tarbar yayan kungiyar kwadago ta NLC, reshen jahar Kano, yayin da suka gudanar da zanga zangar lumana don nuna bacin ransu da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke nukusani wajen mika kudurin dokar sabon tsarin karancin albashin gaban majalisun dokokin Najeriya.

Ganduje yace jahar Kano na daga cikin daddaikun jihohin dake baiwa walwalar ma’aikatanta fifiko ta hanyar biyansu albashi cikin lokaci a Najeriya, don haka yace zasu fara biyan N30,600 da zarar an kamala duk wasu tsare tsaren da suka kamata.

Daga karshe gwamnan yayi kira ga matasa da yan mata da su kauce ma amfani da miyagun kwayoyi saboda matsalar da suke haifarwa ga lafiyan dan adam, wanda daga karshe ka iya sanadin asarar ransu gaba daya.

Shima a nasa jawabin, shugaban NLC reshen jahar Kano, Kabiru Minjibir ya jinjina ma gwamnan jahar Kano bisa kokarin da yake yi ma ma’aikata da kuma alkawarin daya dauka na biyan karancin albashin N30,600 ga ma’aikata.

“Hakan bai bamu mamaki ba, musamman idan aka duba kyakkyawar alakar da kake da ita da kungiyar kwadago, don haka muke kira a gareka da ka taimaka mana wajen shawo kan takwarorinka gwamnoni akan batun biyan sabon karancin albashin."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel