Buhari ya yi tsokaci kan yunkurin juyin mulkin da akayi a Gabon

Buhari ya yi tsokaci kan yunkurin juyin mulkin da akayi a Gabon

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da rundunar sojojin kasar Gabon su mutunta kundin tsarin mulkin kasarsu da kuma demokradiyya.

Shugaban na Najeriya ya yi wannan kirar ne bayan sojojin sunyi yunkurin juyin mulki a kasar ta Afirka mai albarkatun man fetur.

Masu shirya juyin mulkin sun kawace iko da gidan rediyon kasar a safiyar yau Litinin.

Sun fitar da sako inda suka ce shugaban kasar, Ali Bongo bai dace ya cigaba da mulakar kasar ba.

Buhari ya yi tsokaci kan yunkurin juyin mulkin da akayi a Gabon

Buhari ya yi tsokaci kan yunkurin juyin mulkin da akayi a Gabon
Source: Depositphotos

Sai dai jami'an tsaron kasar ta Gabon sun kashe biyu daga cikin wadanda ake zargi da shirya juyin mulkin kuma sun kama mutane bakwai a cewar mai magana da yawun gwamnatin, Guy-Betrand Mapangou.

DUBA WANNAN: Idan Buhari ya fitar da sunayen barayin gwamnati, 'yan Najeriya zasu ji kamar su kashe su - Dan majalisa

"Ya kamata sojojin kasar Gabon su gane cewa zamanin da ake juyin mulkin soja a Afirka da sauran kasashen duniya ya wuce. Demokradiyya shine yafi zama dai-dai kuma dokar kasa ta tanadar da yadda ake canjin gwamnati cikin lafiya. Wannan itace hanyar ta zamu bi domin tabbbatar da zaman lafiya a kasar da nahiyar baki daya," inji Buhari.

Shugaban kasar na Najeriya kansa ya yiwa gwamnatin demokradiya juyin mulki a shekarar 1983 a lokacin yana soja.

Shima daga bisani an yi masa juyin mulkin bayan shekaru biyu.

A sakon da ya aike ga masu shirya juyin mulki, Buhari ya yi kira da sojojin suyi murabus daga mukamansu su shiga siyasa ko kuma su mayar da hankali wurin gudanar da aikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel