An dakatar da sarakuna biyu a Zamfara saboda alaka da 'yan bindiga

An dakatar da sarakuna biyu a Zamfara saboda alaka da 'yan bindiga

Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da hakimai guda biyu da ake zargi taimakawa 'yan bindiga kai hare-hare a jihar Zamfara.

Jihar dai tana fama da hare-hare daga 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane a cikin watannin baya-bayan nan.

Hakiman da aka dakatar suna Bello Mai Wurno na garin Kaya Birnin Magaji da ke karamar hukumar Maradun da Dangaladima Birnin Magaji na garin Birnin Magaji da ke karamar hukumar Birnin Magaji.

Sanarwar ta fito ne daga bakin kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, Bello Magaji a garin Gusau. Ya kuma umurci hakiman su mika kansu ga hukumar tsaro ta NSCDC domin cigaba da bincike.

An dakatar da sarakuna biyu a Zamfara saboda alaka da 'yan bindiga

An dakatar da sarakuna biyu a Zamfara saboda alaka da 'yan bindiga
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Rikici ya barke a wurin kamfen din APC a Legas

Ya ce an gano cewar hakiman suna tallafawa 'yan ta'addan ne ta hanyar taimaka musu da abinci da man fetur.

"Idan ba ku manta ba a kwanakin baya, gwamnatin jihar Zamfara ta haramta sayar da man fetur a bakin titi domin domin rage hare-haren na 'yan bindiga.

"Mun hana sayar da sayar da wasu kayayakin masarufi a wasu kauyukan ne saboda kada 'yan bindigan su samu ikon cigaba da kai hare-hare sai dai abin bakin ciki shine wadannan hakiman su sabawa dokar gwamnati sun bayar da izinin cigaba da sayar da kayayakin," inji kwamishinan.

Ya ce an kuma kama wasu mazauna garin da ke tallafawa 'yan bindigan.

Kwamishinan ya kuma zargi wasu bangare na jami'an 'yan sanda da bawa gwamnati bayannan karya kan ayyukan 'yan bindigan.

"Yan sanda sun bamu bayyanai kan yadda 'yan bindigan ke gudanar da harkokinsu amma daga baya mun gano suna hada baki da 'yan bindigan ne domin ribar da suke samu," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel